Ranar Litinin, ‘Yan sandan Najeriya sunce akalla mutane 80 mabiya addinin kirista wadanda aka yi imanin ‘yan bindiga sun sace su a wasu coci coci uku a arewacin kasar cikin watan jiya, sun koma gidajen su, ikirarin da nan da nan kungiyar kiristoci ta Najeriya ta musanta.
Kamar yadda kungiyar CAN ta fada, yan Bindiga sun kutsa cikin wasu majami’u uku ranar 18 ga watan jiya suka kama mutane 177 suka shige jeji da su da na kusa, 11 daga cikin su suka tsere, sauran mutane 166 a hanun ‘yan binidga.
Kakakin rundunar ‘Yan sanda a jahar kaduna Mansur Hassan, yace sabon Bincike ya nuna cewa mutane 80 da aka bada rahoton sun bace, sun tsere ne zuwa kauyuka da suke kusa lokacin da aka kai musu harin, amma suka dawo gidajen su a kurmin Wali a karshen mako, bayan da suka lura cewa kura ta lafa.
“Ahalin yanzu mun gayyace wadan nan mutane zuwa helkwatar ‘Yansanda a Kaduna domin tantance su, da kuma auna lafiyar su, kamar yadda kakakin rundunar ‘Yan sanda Hassa ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Amma shugaban Kungiyar CAN ta Najeriya reshen jahar Kaduna Rev. Caleb Ma’aji, yace bashi da labarin cewa wasu sun koma gidajen su.


