Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Maganganun Jami’an Shige Da Fice Dana Shugaban Kasa Trump Suna Cin Karo Da Juna
Published: January 28, 2026 at 7:55 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Manyan jami’an shige da fice na kasar Amurka karkashin mulkin Donald Trump sun sha yin bayanai da daga baya hujjoji ke nuna sabanin haka bayan aukuwar mummunar artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan kasa, ciki har da kisan wasu ‘yan kasa biyu a garin Minneapolis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gano.

Jami’an gwamnati sun yi sauri nuna cewa mutane biyu da aka kashe kwanan nan Renee Good da Alex Pretti, sun far ma jami’an tsaro ne da neman halaka su, saboda haka kisan da aka yi musu ya dace. Amma hujja ta bidiyo ta nuna akasin haka, abinda ke kawo shakku wajen mutanen kan ingancin hujjojin jami’an gwamnati.

Abinda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya dubo ya hada da wadannan mutane biyu da aka kashe, da kuma wasu hudu a watannin baya bayannan, inda jami’ai suka yi saurin kare jami’an shige da fice ba tare da sun jira an yi kwakkwaran bincike ba, abinda tsofaffin jami’an shige da fice ke ganin ya sabawa yadda aka saba yi a irin wannan yanayi.

Amurka

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sanda A Jihar Katsina
Next Post: CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025

Karin Labarai Masu Alaka

Akwai Nasara A Tattaunawar Da Akeyi Tsakanin Iran Da Amurka Afrika
Amurka Zata Bada Gudumawar Kudi Dala Bilyan 10 Ga Ayyukan Kwamitin Wanzar Da Zaman Lafiyan Amurka
Amurkawa Sun Nuna Bacin Rai Saboda Yawaita Kashe ‘Yan Kasar Amurka
Shugaba Trump Yace Akwai Yiwuwar Cimma Yarjejeniya Da Iran Afrika
Sabon Ma’aikacin Tsaro Ne Ya Kashe Amurkawa Amurka
Amurka Tafara Yiwa Kasar Iraq Barazana Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza Labarai
  • Mawakiyar Amurka Cardi B. Ta Cashe A Saudi Araibiya Nishadi
  • Shugaban Afrika Ta Kudu Yanuna Goyon Bayan Kawo Karshen Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine Afrika
  • Rasha Ta Nuna Kudurin Cimma Zaman Lafiya Da Ukraine Amurka
  • Mutane Kusan 30 Ne Suka Mutu a Nguru Dake Jihar Yobe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 Najeriya
  • ‘Yan Sandan Birnin New York Sun Karyata Zargin Jefa Bom Ga Masu Zanga Zanga Amurka
  • An Katse Intanet Da Wayar Tarho A Kasar Uganda Siyasa
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.