Majaisar dattawan Amurka yau laraba ta amince da wani gagarumin dokar kudi na samada dala bilyan 901 da ya kunshi manufofin aikin ma’aikatar tsaron Ammurka ta Pentagon. Yanzu za’a aike da dokar zuwa fadar White House, wacce tace shugaba Donald Trump zai sanya hanu akai.
Dokar kasafin kudi na badin, an sami daidaito akai tsakanin wacce majlisar wakilai data dttijai suka amince akansu a bana, dokar ta amince ta kashe dumbin kudaden ta fuskar aikin sojojin kasar nashekara shekara, tareda karawa sojiji albashi da akashi 4, da sayen kayan aikinsu, da kokarin bunkasa rige-rige da Amurkan take yi da kishiyoyinta kasashen Rasha da China.
A wani mataki da ya nuna banbancin ra’ayi tsakanin wakilai ‘yan Republican masu rinjaye a majalisun biyu da shugaba Donald Trump, dokar ta kunshi matakai daban daban na bunkasa tsaro a turai, duk da wani tsari na tsaro da shuggaba Trump ya fitar a baya bayan nan, da ake gani ya nuna sassauci ko dasawa da Rasha, a bangare daya kuma yake sake nazarin dangantakar turai da Amurka.
Ha kazlika dokar ta kunshi kudi dala milyan 800 domin talafawa Ukraine cikin shekaru biyu msu zuwa, kudade da za’a yi amfani da su wajen biiyan kamfanonin da suke kera makamai da Amurka take aikawa Ukraine.
Ahalinda ake ciki kuma, kuri’ar neman jin ra’ayin jama’a, ta nuna cewa farin jinin shugaba Trump yayi baya, yanzu kashi 39 cikin dari na Amurkawa ne suke ganin farinsa. Matsalar tattalin arziki yana daga cikin dalilanda suka sa karbuwarsa tayi baya.
.


