Majalisar wakilan tarayyar Najeriya ta jefa kuri’ar amincewa da sanya baki wajen binciken rikicin da ya barke a tsakanin hukumar kula da jigila da tace danyen man fetur ta Najeriya da matatar mai ta Dangote, a sanadiyyar munakisar bayar da lasisin shiga da tataccen mai cikin kasar, da kuma kayyade farashinsa, yayin da ake zargin shugaban hukumar da wawurar makudan kudade.
Attajirin da ya fi kowa arzikin kudi a Najeriya, Aliko Dangote, ya zargi wannan hukuma da laifin bada lasisin shiga kasar da tataccen man fetur maras kyau da nufin gurgunta matatun tace man fetur na kasar, ciki har da mai tace ganga dubu 650 ta mai a kullum dake Lagos, wadda ita ce kuma mafi girma a duk fadin nahiyar Afirka.
Dangote ya bukaci da a gudanar da bincike akan shugaban hukumar Farouk Ahmed, wanda yayi zargi da rashin iya tafiyar da aiki, da kuma yadda ya kashe dubban miliyoyin Naira wajen tura ‘ya’yansa hudu karatun sakandare a kasar Switzerland, kudin da ba ya da wata hanyar da aka sani ta halal ta samu.
‘Yan majalisa sun yi kashedin cewa wannan rikici a tsakanin Dangote da hukumar yana iya haddasa karancin mai a daidai lokacin da ake tinkarar bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara, kuma tababa a kan hukumar kula da jigila da tace man na barazana ga tabbatar da samuwar makamashi da kashe kwarin guiwar masu zuba jari a fannin.
‘Yan majalisar suka ce matatar mai ta Dangote mai matukar muhimmanci ce ga tabbatar da tsaron makamashi a kasa wadda zata kawo karshen dogaron da Najeriya take yi a kan shigo da tataccen mai, da samarwa da kasar kudaden wajen da take matukar bukata, da ma sauko da farashin mai a cikin gida.
Ba a bayyana ranar da Kwamitin kula da harkokin man fetur na majalisar zai yi zama kan wannan batun ba.


