Najeriya ta amince da biyan kudi Naira biliyan 185 ga kamfanonin samar albarkatun mai da suke bin ta bashi da irin gas da suke samarwa ga injunan samar da wutar lantarki a kasar, domin karfafa bangaren makamashi da inganta samar da wutar lantarki.
Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa dake karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ita ce ta amince da biyan kudin bayan shugaba Bola Tinubu ya bayarda umurnin a biya wadannan basussukan dake neman gurgunta mai da gas da ake bukata ga masana’antun samar da wutar lantarki a kasar.
Karamin ministan man fetur Ekperikpe Ekpo, ya ce za a biya wadannan basussuka ne ta hanyar Zarmiya, wato kamfanonin zasu cire wadannan kudade daga kudaden da ya kamata su biya gwamnati na man da suke dauka daga kasar
Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka, tana ci gaba da fuskantar karancin wutar lantarki da aka kasa shawo kansa shekara da shekaru, abinda ke dakushe harkokin kasuwanci da na tattalin arzikin kasar.


