Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Malami: Gwamnatin APC Ta Gaza – “Yan-Kasa Kuwa Na Da Katin Zabe”
Published: November 24, 2025 at 5:55 AM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: November 24, 2025

Rashin sanin makamar aiki, sakaci da kasawar gwamnatin APC ya kai Najeriya halin da take ciki a yanzu, musamman Arewacin kasar. Kasawar gwamnatin tayi yawa wanda har an kai ga gwamnatocin jihohin yankin rufe makarantun gwamnati.

Wanda hakan babbar koma baya ne ga bangaren ilimi. Arewa na cikin mawuyacin hali musamman a bangaren tsaro, noma, uwa uba ilimi. Arewa bata samu wata riba a cikin wannan gwamnatin. Baki daya idan aka duba za a ga cewar gwamnatin tarayya tare da gwamnatocin jihohi karkashin jagorancin jam’iyyar APC sun gaza samar da tsaro ga al’ummar da suka zabe su.

Don haka al’ummar Najeriya kadai ne zasu iya magance wannan matsalar, na ganin cewar sun fito kwansu da kwarkata da katin zaben su don fitar da wannan gwamnatin daga mulki, muddin kuma ba haka suka yi ba to zasu cigaba da kasancewa cikin ukubar gwamnatin APC. A ra’ayin Malami wanda ke jigo a jam’iyyar adawa ta ADC.

“Na yi iya bakin kokari na rubutawa hukumomi matsayi na don daukar matakan da suka dace tun ba yauba, amma sai aka maida abun siyasa, wasu daga cikin masu kusanci da gwamnati suka ce Abubakar Malami, ya bada bayanan karya, don haka a hukunta shi.

Lallai lokaci ya yi da jama’ar Najeriya zasu fahimci inda wannan gwamnatin tasa gaba, don ba su da tunanin kasar da al’umar ta a gaba.”

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2025/11/Abubakar-Malami-1.mp3
Labarai, Najeriya

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Umurci Janyewa Manyan Mutane ‘Yan Sanda
Next Post: Tabbas Atiku Abubakar Ya Karbi Katin Jam’iyyar ADC

Karin Labarai Masu Alaka

Tinubu Ya Buƙaci Gwamnoni Su Mutunta Hukuncin Kotun Ƙoli Kan ’Yancin Kuɗin ƙananan Hukumomi Labarai
Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Zuwa Jami’ar Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
Kasar Botswana Na Samun Kudaden Shiga Da Lu’ulu’u Labarai
Lauya Bala: Tabbas Kotu Zata Soke Zaben Shugaban PDP, Turaki Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Yadda Aka Yaudari ‘Yan Kasar Ake Tilasta Musu Ayyukan Bauta Afrika
  • Shugaban Guinea-Bissau Umaro Na Fuskantar Matsin Lamba Afrika
  • Allah Ya Yi Wa Sheikh Dahiru Bauchi Rasuwa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 Najeriya
  • Motsepe, Daga 2028 AFCON Zata Sauya Daga Shekaru Biyu Zuwa Hudu Wasanni
  • Burkina Faso: Mun Kama Sojojin Najeriya da Jirgin Yaki Bisa Shigowa Ba Bisa Ka’ida Ba Afrika
  • Trump Yayi Barazanar Goyon Bayan Hari Akan Kasar Iran Labarai
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.