A kalla mutane 26 ne suka rasa rayukan su a wasu hare-hare daban daban guda uku a Nigeria cewar sojoji, da jami’a.
An kashe a kalla mutane 17 ranar Asabar, lokacin da ‘yan bindiga suka farma mazauna unguwar Mbalom a yankin arewacin Gwer a arewacin jihar Benue.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya tabbatar da ahre-haren, amma bai ce ga adadin mutanen da suka rasa rayukan su ba. Mazauna wurin ne suka ce mutane 17 ne suka rasu.
A wani harin daban kuma, a safiyar ranar Asabar da aka kai kan hedkwatar ‘yan sanda a jihar Borno, ‘yan sanda hudu sun rasa rayukan su, bayan sun sha artabu da kungiyar ‘yan ta’adda dake da alaka da kungiyar ISIS, a cewar mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Borno, Kenneth Daso.
A jihar Kaduna kuma, ‘yan bindiga sun hallaka mutane 5 a wani coci, lokacin da suke gudanar da addu’o’in Easter a kauyen Ariko, a cewar sojoji. Ba’a iya gano ko suwaye ‘yan bindigar ba. Sojojin sun ce maharan sun gaza tafiya da mutane 31 da suka yi niyyar garkuwa da su, bayan da dakarun su suka iso gurin domin bada taimako.


