Dr. Usman Isiyaku, mai sharhi akan al’ammuran yau da kullum, shugabanci na gari, ya ayyana wasu kadan daga cikin tsare-tsaren na gwamnatin Tinubu, a kan al’ammurra da suka shafi jagorancin Najeriya.
Inda yake cewa “Bisa ga al’adar gwamnatin Bola Ahmad Tinubu, ba wani abun mamaki bane ko sabon abu, don ya nada Yarbawa, a mafi akasari da mukamai masu girma. Idan aka duba za’a ga cewar tun fara mulkin shi da irin wannan salon ya fara.”
A wasu lokutta kuwa akan ga cewar Arewa tana da girma, don haka idan aka bata wasu tsirarun mukamai sai aga kamar an yi mata wata hikima. Sau da yawa ‘yan Arewa dake tare da gwamnatin ta shi, basu da wani karfi da za su iya gaya mishi gaskiya. Mafi akasari ma ‘yan abi yarima ne a sha kida.
Don kuwa da yawa daga cikin su, ba wai tunanin kasar ne a zukatan su ba, mafi akasari son kansu da nasu ne a zukatansu. Bugu da kari, duk wani abu da za’a gani a wannan gwamnatin, to yana da alaka da gwamnatin da ta gabata, ta Margayi Muhammadu Buhari.
Tsari ne da ba’a la’akari da cancanta wajen zabo wadanda zasu wakilci kasa, ko jama’a. Don haka ba wani abun mamaki bane don anga nadin jakadu na bangaren Yarbawa da basu da kwatankwacin kashi 10 na adadin yawan mutan Arewa, amma suke da jakadu 11 kana aka kai su kasashe manya a duniya.
Inda ita kuma Arewa ta tashi da jakadu 5 daga bangaren Arewa maso yamma, sai 5 daga Arewa maso gabas, kana wasu 5 da ke wakiltar Arewa ta tsakiya. Abun ala’akari a nan shine, yawan mutane da suka fito daga Arewa maso yamma da ke da jihohi 7, sun fi yawan mutane da suka fito daga baki daya Kudu maso Yamma da aka basu jakadu 11.
Haka kuma, wannan gwamnati ce da take la’akari da mutane da suka wahalar mata koda kuwa basu cancanta, da kuma mutane da suka fito daga bangare daya, ko kuwa bangaranci na addini, da na kabilanci, wanda ta haka ne zai ba mutum damar samu wani babban matsayi, ba la’akari da irin gudunmawar da zaka bada ake yi ba.


