Najeriya da kasar Saudi Arabia sun kulla yarjejeniya ta shekaru biyar domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da dangantakar soja tsakanin kasashen biyu.
A cewar wata sanarwa daga ofishin sakataran yaɗa labaran ministan tsaron kasar, Ahmed Dan Wudil, yarjejeniyar za ta haɗa da musayar bayanan leken asiri, horas da soji, ƙera kayan tsaro, da haɗin gwiwa a fagen ayyukan tsaro domin bunƙasa zaman lafiya da tsaron ƙasa.Karamin ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Matawalle, ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Dr Khaleed H. Al-Biyari ya wakilci Saudiyya.
Sanarwar ta ce wannan mataki babban ci gaba ne wajen ƙarfafa hulɗa, inganta haɗin kai da kuma yaki da sabbin kalubalen tsaro dake tasowa a yankin.


