Najeriya Ta Gabatar Da Tayin Karbar Bakuncin Wasannin Afirka na 2031N
Najeriya ta gabatar da bukatarta ga Majalisar Wasannin Tarayyar Afirka (AUSC) a hukumance don karbar bakuncin Wasannin Afirka na 2031, wanda hakan ke nuna burin kasar na sake maraba da babban taron wasanni na Afirka, kusan shekaru 25 bayan karbar bakuncin da tayi 2003 (COJA).

An gabatar da tayin ne a lokacin manyan taruka da AUSC, inda Najeriya ta sake tabbatar da shirye-shiryenta da karfinta na shirya wani kasaitatcen bikin na musamman wadda Mainasara Ilo, ya gabatar da tayin ga AUSC.
Najeriya ta na da kwarewa ta musamman ta hanyar karbar bakuncin manyan tarukan wasanni na kasa da kasa.
Wadan da sun hada da Gasar Wasannin Athletic U18/U20 ta CAA, Gasar Karate ta Afirka, Gasar Tennis ta Matasan Afirka ta ITTF, Gasar Kokawar Hannu ta Afirka, Gasar Badminton, Wasannin Para Game, na Yammacin Afirka, da Gasar Cadet da Junior Taekwondo ta Afirka, da sauransu.
Waɗannan nasarorin sun nuna ci gaba da shirin ƙasar na ɗaukar nauyin shirya wani taron da ya yi daidai da girman Wasannin Afirka.

Muhimmin abin da ke ƙara tasiri ga ci gaban wasannin nahiyar shi ne Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC), Malam Shehu Dikko, da Darakta Janar, Hon. Bukola Olopade, waɗanda suka ci gaba da kare ajandar tattalin arzikin wasanni ta Najeriya.
Jagorancinsu ya haifar da manyan gyare-gyare da saka hannun jari waɗanda suka riga suka samar da sakamako mai kyau.
Nasarar da Najeriya ta samu wajen karɓar bakuncin gasar wasannin motsa jiki ta Afirka ta CAA U18/U20 ta haifar da babban tasiri ga tattalin arziki, wanda ke ƙarfafa ayyuka masu yawa sama da ƙananan da matsakaitan kamfanoni (SMEs) 5,000 sun amfana da ƙaruwar tallafi, wanda ya haifar da karin kuɗi mai yawa ga tattalin arzikin yankin.
Hakazalika, gasar tsere Access Bank Lagos City Marathon, wacce aka amince da ita a matsayin gasar Athletics Gold ta duniya, ta zama babban abin nuni ga Najeriya – tana haɓaka yawon buɗe ido, da kuma jawo hankalin manyan mutane daga ko’ina cikin duniya.
Najeriya ta kuma karɓi baƙuncin Gasar Wasannin Sojojin Afirka ta 2024, Africa Military Games, wani taron da ya ƙarfafa ƙarfin ƙasa ya ƙara haɗin gwiwa a yankin, da kuma ci gaba da diflomasiyyar soja a nahiyar.
Bugu da ƙari, Wasannin Para Games na Yammacin Afirka da wasu taruka da suka shafi wannan gasa da aka shirya a ƙasar sun samar da ɗaruruwan ayyukan yi kai tsaye inda da suka shafi dubban mutane a fannoni kamar su karɓar baƙi, sufuri, yawon buɗe ido, tsaro, sayar da kayayyaki, da ayyukan taruka.
Ƙoƙarin Najeriya na karɓar bakuncin Wasannin Afirka na 2031, African Games, yana ƙarƙashin jagorancin hangen nesa na gaba don amfani da wasanni a matsayin abin ƙarfafa ci gaban ƙasa.
Wasanni sun kasance aiki mai ƙarfi wajan haɓaka haɗin kai, ƙarfafa matasa, da ci gaban ƙasa.
.


