Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Zata Tabbatar Da Tsagaita Wuta A Kwango
Published: February 3, 2026 at 9:40 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta ce cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Kwango, zata tura tawagarta ta farko da zata sa ido kan tsagaita wuta tsakanin gwamnatin Kwango da kungiyar ‘yan tawayen kasar da ake kira da lakabin AFC/M23. Ma’aikatar ta bayyana haka ne ranar Litinin, bayan da ta jagoranci zaman shawarwari a Doha.

Qatar tace tawagar ta MDD zata girke ne a Uvira wani wuri mai muhimmanci a gabashin Kwango, da ‘yan tawayen kasar suka kama cikin watan Disamba bara, lokacin da suka danno kamar guguwa suna ta kama wurare, birni da dakarun kasar ta Kwango suka sake shiga da cikin watan jiya bayanda ‘yan tawayen suka ce za su janye.

Sanarwar da Qatar ta bayar a daren ranar litinin, alama ce ta ana samun ci gaba a shawarwarin da Doha take shiga tsakani ana gudanarwa tsakanin Kwangon da ‘yan tawayen na M23, wadanda a bara suka kama kasa da bata taba rikewa ba gabashin Kwango.

A gefe daya kuma Amurka tana shiga tsakani a wani zaman shawarwari tsakanin Kwangon, da kuma Rwanda, wacce MDD da manyan kasashen yammacin duniya suka ce itace uwargijiyar M23, zargi da hukumomin kasar a Kigali suka musanta.

Yunkuri na baya bayan na farfado da shirin sa ido kan yarjejeniyar tsagaita wutan ya biyo bayan ci gaba da gwabza fada a gabashin Kwangon.

Ahalinda a ke ciki kuma, kudin inshora na gudanar da harkokin kasuwanci a Kwangon ya tashi ninkin ba-ninkin, kamar yadda masu aikin sayar da inshora suka gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Shugaba Trump Yace Amurka Da Iran Suna Cigaba Da Tattaunawa
Next Post: Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Namibiya Tayi Watsi Da Yarjejeniya Tsakanin Ta Da Kamfanin Total Labarai
Rundunar Sojin Iran Tace Harin Amurka Ya Kashe Musu Sama Da Mutane Dari Afrika
Sanyin Hunturu Yayi Ajalin ‘Yan Cirani A Morocco Afrika
Tinubu: Sojojin Mu Sun Yi Rawar Gani Don Kare Demokuraɗiyya A Jamhuriyar Binin Labarai
Iran Ta Kama Wasu ‘Yan Leken Asiri Afrika
An Sako Dan Siyasar Kasar Venezuela Daga Gidan Yari Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
  • Sakataren Gwamnatin Amurka Ya Bayyana Bawa Kungiyoyin Agaji Damar Kai Taimako Sudan Amurka
  • Shugabannin Sojojin Najeriya sun Kai Ziyarar Aiki Maiduguri  Afrika
  • Okoye Na Shirin Maye Gurbin Nwabali, AFCON 2025: Wasanni
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana Afrika
  • Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana Labarai
  • Domin Inganta Tsaro Najeriya Ta Sayi Jiragen Yaki A Kasar Italiya Tsaro
  • Anyi Girgizar Kasa Mai Karfi A Kasar Mexico Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.