Mataimakin Shugaban jami’ar jihar Gombe Ferfesa Sani Yauta ya kaddamar da littafi mai take Sauye-Sauye a bangaren ilimi da shugabanci.
Jami’ar Gombe (GSU) ta gudanar da bikin kaddamar da sabon littafi mai suna “Dynamics of Educational Administration and Planning” wanda Farfesa Sani Ahmed Yauta ya rubuta, a dakin taro na Haruna Kadir Rasheed dake jami’ar.
Taron ya sami halartar jami’an gwamnati, malamai, da baki na musamman.
Shugaban taron, mataimakin Gwamnan Jihar Gombe, Dr. Manassah Daniel Jatau, ya yabawa Farfesa Yauta bisa wannan gudummawar ilimi da ya bayar a sashin ilimi.

Fitattun jami’an gwamnati sun halarci bikin, ciki har da shugaban ma’aikata na jihar Gombe, Alhaji Ahmed Kasimu Abdullahi, Shugaban Jami’ar Tarayya dake Kashere, Farfesa Umaru Pate, Shugaban Jami’ar Lincoln University, Farfesa Adamu Sadiq Abubakar da Shugabar kwalejin koyon jinya, tare da wasu shugabannin cibiyoyi a jihar.
Haka zalika, Daraktan Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH), Farfesa Yusuf Muhammed Abdullahi, ya hallarci bikin tare da sauran manyan baki.
A jawabin sa, Babban Mai Kaddamarwa, Arc. Yunusa Yakubu, ya jinjina wa Farfesa Yauta kan jajircewarsa wajen bunkasa ilimi, yana mai bayyana littafin a matsayin abin dogaro ga masu gudanarwa, masu bincike da masu tsara manufofin ilimi.
Littafin dai wata dama ce da mahukunta zasu iya amfani da ita don sabutan tsari da manhajoji da ake amfani da su a makarantu a kasar baki daya. An kuma ja hankalin sauran malamai a fannin ilimi da su bada irin wadannan gudumawar don habaka ilimi, da ganin an samar da yanayi wanda ilimi a kasar zai yi gogayya da kasashe masu cigaba a fanin ilimi.
Kabatar da kasidu da taron karawa juna sani irin wadannan na da matukara muhimanci ga cigaban ilimi, ta haka ma ana iya sako daliban ilimi wajen shirya irin wadannan tarukan, da muna musu makamar aiki; a cewar daya daga cikin mahalarta taron.


