Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna Afrika
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi Afrika
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Taya Sarkin Musulmi Murnar Cika Shekaru 70, Ya Yi Masa Addu’ar Ƙarin Lafiya Da Tsawon Rai Afrika
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika

Sabuwar Sakatariyar Ƙungiyar Gwamnonin Arewa Za Ta Ƙarfafa Ayyukan Ci Gaban Yankin
Published: July 10, 2026 at 9:49 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya kuma Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da sakatariyar wucin gadi ta ƙungiyar a birnin Kaduna, tare da yin kira ga shugabannin Arewa da su ƙara haɗa kai domin magance matsalolin tsaro, tattalin arziki da ci gaban da yankin ke fuskanta.

An ƙaddamar da sakatariyar ne a gini mai lamba 26 da ke kan titin Muhammadu Buhari Way, tsohuwar WAFF Road, inda kuma aka miƙa motocin aiki domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan ƙungiyar.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa kafa sakatariyar wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa ayyukan ƙungiyar da samar da ingantaccen tsari na daidaita manufofi da shirye-shiryen ci gaban jihohin Arewa 19.

Ya ce lokaci ya yi da shugabannin Arewa za su gina kan kyawawan tubalan da magabatan yankin suka kafa, tare da nuna jajircewa da sadaukarwa wajen magance ƙalubalen da yankin ke fuskanta.

Gwamnan ya jaddada cewa halin da Arewa ke ciki na buƙatar haɗin kai da ɗaukar matakai cikin gaggawa, yana mai bayyana cewa aiwatar da tsare-tsaren da ƙungiyar ta tsara zai taimaka wajen shawo kan matsalolin yankin.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris, ya sake tabbatar da aniyar gwamnonin Arewa na ci gaba da haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tunkarar matsalolin yankin. Ya kuma yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa jagorancinsa wanda ya haifar da kafa sakatariyar ƙungiyar.

Shi ma Babban Daraktan Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Dakta Ezekiel Gomos, ya ce sabuwar sakatariyar za ta inganta gudanar da ayyuka, daidaita manufofi da shirye-shiryen ƙungiyar, tare da ƙara inganta haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar da sauran hukumomin yankin da na ƙasa.

Ya gode wa Gwamna Inuwa Yahaya da sauran gwamnonin Arewa bisa goyon bayan da suka bayar, yana mai tabbatar da cewa za a yi amfani da sakatariyar da motocin aikin cikin gaskiya da inganci domin cimma manufofin ƙungiyar.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Siyasa, Tsaro

Post navigation

Previous Post: TIC Dutse Ta Nemi Ƙarin Tallafin Gwamnatin Jigawa Don Faɗaɗa Ayyukanta
Next Post: APC: Tinubu Da Shettima Za Su Sake Neman Wa’adi Na Biyu A 2027

Karin Labarai Masu Alaka

Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Afrika
Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York Afrika
An Gurfaranar Da Wadanda Ake Zargi Takai Hari Gaban Kotu Najeriya
Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Ya Rasu A Abuja Bayan Doguwar Jinya Afrika
Amurka Ta Girke Jirage Marasa Matuki Tare Da Sojoji A Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Fanny Amun Ya Yi Murabus A Matsayin Shugaban Kwamitin Binciken NFF
  • Pasto Yohanna Buru Ya Jagoranci Kiristoci Wajen Bikin Mauludi Tare Da Musulmi A Kaduna
  • Tinubu Ya Buƙaci Musulmi Su Riƙe Haƙuri, Tawali’u Da Tausayi
  • Ceferin Ya Ce Ba Zai Yi Takarar Shugabancin FIFA Ba
  • Maulidin 2026: IMC Ta Yi Kira Da Ƙarfafa Zaman Lafiya Da Haɗin Kai A Najeriya

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Eberechi Eze Ba Zai Buga Wasannin Da Ingila Za Tayiba Arteta Wasanni
  • An Gabatar Da Sabbin Kudurorin Kare Muhalli Da Gandun Daji A Gombe Afrika
  • Farashin Man Fetur Yakara Tashi Labarai
  • Sojojin Da Suka Kifar Da Farar Hula A Guinea-Bissau Sun Sanar Da Cewa! Afrika
  • An Kaddamar Da Kwamitin Kwallon Kafa A Tsakanin Masarautun Jihar Gombe Labarai
  • Kimanin Ganga Miliyan 40 Na Danyen Albarkatun Mai Yayi Kwantai A Kasashen Afirka Ta Yamma Afrika
  • Arsenal Tana Ci Gaba Da Kokarin Dauko Morgan Rogers Wasanni
  • Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.