Babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Mark Rutte, yayi magana da wasu hukumomi na kasashe dake suke cikin kungiyar tsaro ta NATO cewa shugaba Trump yana son ganin shirye shirye kwarara cikin ‘yan kwanaki na kare mashigin ruwan Hormuz, kamar yadda wasu jami’an difilomasiyya uku daga turai suka gayawa kamfanin dilancin labarai na Reuters a jiya Alhamis.
Ranar Laraba ne Rutte ya gana da Donald Trump a Washington, yayinda ake zaman tankiya ko dar dar cikin kungiyar kan yaki kan Iran.
“Babban sakataren yana magana da kasashe da suke cikin kungiyar dangane da shawarwari da yayi da hukumomi a Washington,” inji kakakin kungiyar Allisonn Hart, a ranar Alhamis, ta kara da cewa “a bayyane yake Amurka tana son ganin an dauki matakai kwarara domin tabbatar da ganin zirga zirga ba tareda tsangwama ba mashigin ruwan Hormuz.”
Shugaban na Amurka ya sha kiran kungiyar NATO a zaman dodon bango, har yayi barazanar zai janye Amurka daga cikin Kungiyar mai wakilai 32 a kalamansa cikin makonnin baya bayan nan, yana mai cewa turai ta dogaro ne kan tsaron da Amurka take bata, yayinda kasashe da suke cikin kungiyar suka kasa bada wata gudumawa ta kwarai, a artabun da Amurka da Isra’ila suke yi da Iran.


