Sabon Shugaban ƙungiyar Kwallon Kafa ta Wikki Tourist FC Bauchi dake tarayyar Najeriya Salmanu Abubakar yayi alkawarin kawo ci gaba a ƙungiyar.
Salmanu Abubakar ya ce tun kafin ya zo wannan matsayi dama ya san matsalolinta, domin ya rike matsayin Sakataren ƙungiyar magoya bayan Wikki.
Babban matsalar Wikki shine shishigi wajan shiga aikin da ba naka ba “in ji shi, a lokacin zantawarsu da wakilin GTA Hausa.
Saboda haka babban abunda ya farayi shine zama da ma’aikatan hukumar don gyara wannan lamari ta hanyar ko wa ya tsaya akan aikin sa, abunda bature ya ke ciwa (Division of labour) yin haka shine mataki gyara na farko wadda hakan zai kawo cigaba sosai.
Kan batun ‘yan wasa kuwa Salmanu yace ya dauki matakin gyara tun da dama rashin sanya kwallon a raga ita ce matsala to tuni ya gayyaci sabbin ‘yan wasa shida da zai’yi anfani da su a tsakiyar kakan wanan bana kuma kwaliya zata biya kudin sabulu wajan faranta wa magoya baya rai.
Ya kuma bada tabbacin zasu ba wa maihoras da ƙungiyar Abdullahi Maikaba, cikekken dama wajan gudanar da aikin sa don samun nasara wa ƙungiyar.
Salmanu yace kamar yadda maigirma Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Muhammad, ya basu amana don gyara da kuma kawo cigaba a wannan Ƙungiyar to bazasu ci amanan maigirma Gwamnan ba wajan aiki tukuru don samun nasara a wannan Ƙungiyar ta Wikki Tourist FC.
Da ya ke tsokaci ga me da ƙungiyar magoya bayan Wikki Tourist, Salmanu Abubakar ya ce wannan shine babban kalu balen sa amman akwai shiri da yakeyi don tabbacin adalci a duk bangarorin jihar Bauchi wajan sanya musu wakili a cikin wannan ƙungiya, bayan haka akwai wata horaswa ta musamman da za’a basu wajan yadda zasu gudanar da aikin yayin wasanni.
Daga karshe yayi alkawarin dawo da ƙungiyar cikin hayyacinta a teburin gasar Firimiyar lig na Najeriya ganin yadda kungiyar a yanzu ta ke wani matsayi da bai da ce ba.


