A yau abinda ke faruwa game da yakin Amurka, Isra’ila da Iran, kudin man fetur ya haura dala 100 kowacce ganga saboda ci gaba da kulle mashigin ruwa na Hormuz da Iran ke yi, tare da kuma far ma duk wani jirgi da ya nemi wucewa ta wajen.
Sannan Iran din kuma ta dau alwashin daukan fansar mutanen ta da aka kashe. Sabon shugaban addini, Ayatollah Mojtaba Khameni ya ce banda mahaifin sa, ya rasa matar sa da ‘yar uwar sa tare da ‘yar ta karama da kuma surikin sa, a jawabin sa na farko da ya yi bayan nada shi. Ya kuma ce za’a ci gaba da rufe mashigin ruwa na Hormuz.
A Amurka Jami’an gwamnati sun kiyasta a kwanaki shida da aka yi ana Tafka yaki da Iran an kashe a kalla dala miliyan dubu goma sha daya da miliyan dari uku, yayin wani taron majalisa a wannan makon.
Ita kuma hukumar makamashi ta duniya wato IEAE ta ce yakin ya kawo hargitsi mafi girma a tarihi ga samar da makamashi a duniya.


