Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Kagarko Alhaji Sa’ad Abubakar rasuwa a yau Alhamis.
Ya rasu yana mai shekara 110.
Za a gudanar da jana’izar sa a gobe Juma’a bayan Sallar Juma’ah a Masallacin kofar Fadar sa dake Kagarko, jihar Kaduna a Najeriya.
Basaraken Ya Rasu bayan fama jinya a Wani asibiti a Kaduna.


