Bayan wafatin Sheikh Dahiru.
Tun bayan rasuwan Mashahurin Malamin addinin Musulunci nan kuma daya daga cikin Khalifofin Shehu Ibrahim Inyass, wato Sheikh Dahiru Usman Bauchi Al’ummar Musulmi Daga cikin da wajen Nijeriya sunci gaba da zuwa ta’aziyya.
Kuma Babban abinda Al’umma suka fi damuwa dashi shine Yaya Zaayi wannan tafiyar da ya xora Al’ummar Musulmi a kai taci gaba,
Kamar yadda yake a al’adar Shehunnan Dariqar Tijjaniyya da ma maluma a Duniya ,Idan Malami ya rasu Akan duba daya daga cikin Yayansa Na jini Ko Na Ruhi a Dora musu jagoranci na tafiyar da kulawa da Al’umma.
Bayan Rasuwan Sheikh Dahiru Usman Bauchi,Babban Dansa Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru shine khalifan Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Manyan Malamai da dama dasu kazo ta’aziyya sunyi nasiha wa Yaya DA almajiran Sheikh Dahiru dasuyiwa. Khalifan shehin biyayya. Wanda Yi masa biyayya shine aikin da Duk masoyin Shehu Na gaskiya zaiyi.
Sun Kuma to masa adduoi Na cewa Allah ya masa jagoranci , Kuma ya taimakeshi tafiyar da Al’umma.
Cikin Jawaban da yayi Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru ya bayyana cewa Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh Al Hussain shine Jagorar Dariqar Tijjaniyya,Kuma duk abinda zasuyi Sai sun Nemi izininsa.

Yace dama su biyune suka rage cikin khalifofin Shehu Ibrahim,tunda Shehu ya rasu yanzu saura Maulana Sheriff, duk abinda zamuyi Sai mun nemi izininsa, tun Shehu yana raye kullum zamuyi Abu in Mun nemi izininsa ya kance mana muje mu fadawa Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh yace Duk Inda yake shima anan yake.

