Shugaba Trump na Amurka ya bada umurnin a tare dukkan jiragen ruwan dakon mai da aka sanya ma takunkumi a hana su shiga Venezuela, a wani matakin da ake dauka a zaman karin matsin lamba a kan shugaba Nicolas Maduro da kuma takura tattalin arzikin kasar.
Wannan umurni na shugaba Trump yana zuwa a bayan da sojojin Amurka suka kama wani jirgin ruwan jigilar man fetur a makon da ya shige a kusa da gabar kasar Venezuela, a bayan da Amurka ta girka sojoji masu yawa a yankin.
A cikin bayanin da yayi a shafinsa na sada zumunta ranar talata, shugaba Trump yayi zargin cewa Venezuela tana amfani da kudin mai wajen karfafa safarar muggan kwayoyi da wasu laifuffukan, yana mai lasar takobin ci gaba da matsin lambar soja har sai kasar Venezuela ta mayar ma Amurka a cewarsa Mai da kasa da kuma kadarorinta.
Abinda ba a fahimta a wannan bayani na shugaban ba shine wane irin hakki Amurka take da shi a game da man fetur ko kasa ko kuma kadara na Venezuela.
Shugaba Nicolas Maduro ya yaba ma ‘yan kasarsa da yace an shafe makonni 25 ana neman firgita su da nuna musu yatsa.
Trump yace duk wannan matsin da ake yi na neman hana safarar muggan kwayoyi zuwa Amurka ne, amma kuma shugabar ma’aikatan sa Susie Wiles ta fada cikin wata hirar da aka wallafa ranar talata a mujallar Vanity cewa wannan matsi wani yunkuri ne na kawar da shugaba Maduro daga kan mulki.
Kasar venezuela ta fi kowace kasa a duniya arzikin man fetur.


