Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika sunan tsohon shugaban rundunar sojin kasa, Janar Abdulrahman Dambazau (rtd) da kuma tsohon shugaban mulkin rikon kwarya na Jihar Rivers, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (rtd), domin nada su a matsayin jakadu a sabon jerin sunayen da aka tura wa Majalisar Dattawa.
Tinubu, wanda a baya ya tura sunayen jakadu 32, yanzu ya ƙara sunaye 35, wanda hakan ya kai jimillar 65 da ya aika domin tantancewa da tabbatarwa.
A cikin jerin, akwai 34 masu sana’ar diflomasiyya (career ambassadors) da kuma 31 da ba ‘yan diflomasiyya bane kai tsaye (non-career ambassadors


