Shugaban Amurka, Donald Trump ya bukaci ‘yan Iran da su ci gaba da zanga-zanga, kuma su tuna da sunayen mutanen da ke gallaza musu, inda ya ce taimako na tafe, yayin da hukumomin Iran ke ci gaba da tsaurara matakai a kan su.
Trump ya ce ya soke duk wata tattaunawa da jami’an Iran har sai an tsagaita wannan kisa mara kan gado da ake yi wa mutane.
‘Yan gwagwarmayar adawa na kasar Iran a Rome dake kasar Italiya sun zanta da kamfanin dillacin labarai na Reuters game da halin da ake ciki na rikicin siyasa a kasar su, inda suka nuna damuwar su game da halin mutane ke ciki.
Wani dan gwagwarmaya, wanda yake dalibi ne daga Iran, da kuma ya nemi a boye sunan sa, ya nuna yadda abin yayi tsamari, inda yayi bayanin cewa duk mutanen, kama me kudi da talaka, yaro da babba, sun fito zanga-zanga kuma ya ce mutanen sun fusata ainun.

Hukumomin Iran sun ce, a kalla mutane 200 suka rasa rayukan su.


