Ranar lahadi idan Allah ya kai mu shugaban China Xi Jinpin, zai karbi bakuncin takwaran aikin sa na Korea ta kudu Lee Jae Myung, wanda zai kai ziyarar aiki, matakin da yake nuna kokarin hukumomi a Beijing na karfafa dangantaka da Korea ta kudu, yayinda dangantakar ta da Japan yayi tsami kan makomar Taiwan.
Ziyarar itace karo na biyu da shugaba Xi zai gana da Lee a cikin watanni biyu, ba safai hakan ke faruwa ba, wanda yake nuna kudurin China na ganin ta inganta dangantaka, da bunkaa harkokin tattalin arziki da yawon bude ido tsakanin kasashen biyu.
Dangantaka tsakanin China da Japan yayi tsami bayanda PM Japan tace idan a misali, China ta kai hari kan Taiwan, matakin zai tilastawa Japan ta maida martani na soja da hukumoin kasar dake Tokyo za su yi.
Masu fashin baki suka ce gayyatar da shugaba Xi ya yi wa takwaransa na korea ta kudu wata hikima ce ta bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu, gabannin ziyarar da shugaban na Korea ta kudu zai kai Japan nan gaba.
A halin da ake ciki kuma, shugaban Taiwan Lai Chingte, ranar Alhamis yace tsibirinn ya lashi takobin kare ‘yancin ta, tare da karfafa matakan tsaro, bayan da Beijing ta harba makaman rokoki ta kan tsibirin, a wani mataki na rawar daji da Chinan tayi a ‘yan kwanakin nan.


