Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugabannin Sojojin Najeriya sun Kai Ziyarar Aiki Maiduguri 
Published: March 18, 2026 at 1:52 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: March 18, 2026

Shugabannin Sojojin Najeriya sun Kai Ziyarar Aiki Maiduguri

Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar O.O Oluyede, da Babban Hafsan Rundunar Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, sun isa birnin Maiduguri na Jihar Borno domin shaida yanayin da ake ciki na matsalar tsaro da kuma jajantawa al’ummar jihar Borno.

Ziyarar tasu na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar na tura dukkan hafsoshin tsaro zuwa Maiduguri, sakamakon jerin hare-haren ƴan ta’adda, ciki har da fashewar bama-bamai guda uku a yammacin ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 20 tare da jikkata fiye da 100.

Shugabannin sojojin sun sauƙa a sansanin sojin sama da ke Maiduguri, inda kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta yankin Arewa maso Gabas (Operation Hadin Kai), da sauran manyan hafsoshin soji suka karɓe su.

Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na magance ƙaruwar hare-haren ƴan ta’adda a jihar Borno, musamman bayan hare-haren bama-bamai na baya-bayan nan da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP ne suka kai.

Tun da farko dai, Shugaba Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren, inda ya bayyana su a matsayin “ayyukan mugunta na ƙungiyoyin ta’addanci masu muguwar aniya,” tare da alƙawarin ƙara ƙaimi wajen yaƙar dukkan ƙungiyoyin ƴan ta’adda.

A halin yanzu, rundunar soji na ci gaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya da tsaro mai inganci a yankunan da abin ya shafa, ta hanyar ƙara sa ido da kuma ƙarfafa matakan tsaro.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Tinubu Ya Bayyana ‘Yan Bindiga Da Cewa Ruwa Yakarewa Dan Kada
Next Post: Kasar Saudiya Zata Cika Azumi Talatin

Karin Labarai Masu Alaka

Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka Afrika
Ga Fili Ga Doki Najeriya
Prime Ministan Senegal Ya Bayyana Shirin Sauya Sheka Afrika
Muna Kira Ga Kasashen Duniya Su Sa Baki Don A Saki Mohamed Bazoum Afrika
Jirgin Ruwan ‘Yan Gudun Hijira Ya Nitse Kogi A Tunisiya Labarai
Dottin Shara Ya Damu Jama’ar Havana Kasar Cuba Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sarkin Gombe Ya Ziyarci Gwamna Inuwa Yahaya Afrika
  • Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
  • Magoya Bayan Nice Sun Kai Hari Wa ‘Yan Wasansu Wasanni
  • Magoya Bayan Obi Sun Yi Tutsu Gabanin Zaben 2027 Siyasa
  • Sojoji Sunkai Farmaki Gidan Dan Adawa A Kasar Uganda Bobi Wine Afrika
  • ‘Yan-Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Daliban St. Mary! Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • CAF Ta Yanke Hukunci Kan Ƙasashen Senegal Da Moroko AFCON 2025 Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kungiyar Kwallon Mata Sun Tsallaka Iyakar Turkiyya Zuwa Iran Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.