Sojojin sama a Nigeria sun yin nasarar lalata jiragen kwale-kwale 10, tare da hallaka ‘yan ta’adda 40, dake shirin kai hare-hare a jihar Borno, a cewar sojojin a jihar ranar Lahadi. Wannan na daya daga cikin samamen da sojojin ke kaiwa yankunan da ke kewaye da kogin Chadi don dakile shirin ‘yan ta’adda.
Mai magana da yawun sojin sama, Ehimen Ejodame ya ce harin da aka kai ta jiragen sama kan mafakar Musarram da Azir, yana nuni ka kara matsin soja ga ‘yan ta’adda dake yawan amfani da yankunan saboda sarkakiyar su da yawan duwatsun su don kwanton bauna wajen kaiwa dakarun soji da kuma mazauna kusa da yankunan hari.
Ya ce sun samun nasarar tarwatsa ‘yan ta’addan, tare da hallaka da dama a Musarram, bayan da suka samu bayanan sirri cewa sun yi gangami cikin kwale kwale don kai hari zuwa garin Baga da dam din da ake kamun kifi a yankin tafkin Chadi.
A Azir kuma, jirgin yakin sojin sama ya harbo ‘yan ta’addan yayin da suke kokarin tserewa bayan gobzawa da dakarun tsaro ranar Jumu’a, inda nan ma aka kashe da daman su.


