Ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Muhammad Jibrin Barde, ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) gabanin zaɓen 2027.

Dan Barde ya bayyana hakan a daren ranar Talata a gidansa, inda ya nuna katin zamowa mamba na ADC, yana mai cewa ya dawo ne domin sabunta rajistar sa da jama’rsa
Ya ce ya bar PDP tun farkon shekarar 2025, yana jaddada cewa burinsa shi ne ceto jihar Gombe daga abin da ya bayyana a matsayin mulkin masu harkar kasuwanci.
“Ina tabbatar muku da cewa, kamar yadda kuka sani, ana samun gagarumar tafiya a faɗin ƙasar nan, wadda muka ba wa suna ‘Salon Tafiya’.
“Muna aiki a kan wannan tafiya tare da shugabanninmu a faɗin ƙasar, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, tsofaffin gwamnoni da ministoci.
“Manufar wannan tafiya ita ce ceto ƙasar nan daga halin da take ciki na rashin tsaro, matsin tattalin arziki da ƙarancin ababen more rayuwa,” in ji shi.
Jibrin Dan Barde ya ƙara da cewa, “Yana da muhimmanci mu dawo gida domin sabunta rajistar membobimmu kuma mun kuduri aniyar ci gaba da wannan tafiya, kuma yanzu ne lokacin da ya dace mu sake sabunta membobimmu.”
Dangane da haɗin kai, ya ce hadakar ta himmatu matuƙa wajen ceto jihar, yana nuna damuwa kan lalacewar ababen more rayuwa da kuma ƙaruwar rashin tsaro.
“Kamar yadda kuke gani, akwai ƙarancin ababen more rayuwa da kuma rashin tsaro, sannan wannan shine iri rashin ɗaukar alhaki ne muke son yaƙi a jihar nan.
“Muna son samar da shugabanci mai ma’ana, mu bai wa kowa damar cin nasara, mu inganta ilimi ba ilimin da mutum ɗaya ko ƙungiya ke sarrafawa kamar kamfani mai iyaka ba,” in ji shi.
Da yake bayyana dalilin komawa ADC, Dan Barde ya ce jam’iyyar na wakiltar sabon zamani, tare da kira ga wasu da su shigo cikinta.
“Abin da muke son yi yanzu shi ne sabunta membobimmu a ƙarƙashin sabon zamani, kuma ga waɗanda ba mambobi ba, muna kiran su da su shigo ADC domin mu tunkari wannan gwamnati mai ɗaukar alhaki,” in ji shi.
Haka kuma ya gargaɗi al’umma da kada su sayar da ƙuri’un su.
“Kada ku karɓi taliya ko Naira 500 ku sayar da ƙuri’unku yace waɗannan darussa ne masu muhimmanci da ya kamata mu koya


