Shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyib Erdogan ya ce a ranar Talata, yarda da Isara’ila ta yi da Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kan ta ba zai amfani ita kan ta Somaliland din ko kuma yankin da ta tsage daga ciki ba.
Tun a watan Disambar bara ma shugaban na Turkiyya yayi irin wannan martani inda ya ce shawarar da Isra’ila ta yanke na yarda da Somaliland, wadda ke a yankin arewacin Somalia, da ta yi ikirarin samun ‘yancin kai a matsayin kasa mai cin gashin kan ta a shekarar 1991, ya sabawa doka, ya kuma zargi Isra’ila da son kawo hargitsi a yankin na Afirka.
Turkiyya, wadda ke cikin kungiyar kasashen NATO tana kara tasirin ta a kasashen Afirka a shekarun kwana kwanan nan, inda ta ke horar da jami’an tsaron Somalia, tare da samar da taimakon kawo ci gaban kasa, a madadin bata damar amfani da hanya mai muhimmanci ta fitar da kayyayaki. Yayin da ita kuma kasar Somalia ta Yanke duk wata alaka dake tsakanin ta da kasashen Haddaddiyar Daular Laraba, inda ta zarge su da yin tasiri wajen yarda da Somaliland da Isra’ila ta yi a matsayin kasa mai ‘yancin kai.


