Ukraine ta mikawa Amurka daftarin yarjejeniyar kawo karshen yakin da kasar take yi da Rasha da aka yi wa kwaskwarima mai bukatu ko matakai 20, kaar yadda shugaban na Ukraine Volodymyr Zelensky ya fada yau Alhamis, ya kara da cewa har yanzu batun baiwa Rasha wani bangaren kasar yana ci gaba da hana ruwa gudu a shawarwarin.
Da yake magana da manema labarai a Kyiv, Zelensky, yace domin a sami daidaito, Amurka tayi alkawarin zata bude harkar kasuwanci a gabashin bangaren Donbas da Ukraine take iko akai, wadda Rasha ta nemi Ukraine ta bar mata.
Yace, a ganin Amurka, idan sojojin Ukraine suka janye daga yankin Donesk, yarjejeniyar itace Rasha ba zata shiga yankin ba. Sai dai basu san wai mallaki iko akan yankin ba. Rasha tana so a akalli yankin a zaman wuri da ba za’a ayyana yaki ba.
Zelensky yace har yanzu ba’a sami fahimta kan batun mallakar iko kan yanki ko sassa, ya kara da cewa tilas ‘yan kasar su kada kuri’a raba gardama kan duk wata bukatar Ukraine ta rasa wani bnagren kasarta.
Ahalinda ake ciki kuma shugaban Rasha Putin ya godea dakarun ksar, bayanda kwamandoji suka bashi rahton cewa dakarun Rash su kama garnda ake kira Siversk, amma sojojin Ukraine suka ce har yanzu su suke da iko kan wannan gari.


