A yau Litinin 1 ga watan Disamba 2025 an fafata a Babban wasan Hamayya, Super Lig Istanbul Derby
Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1
Galatasaray da Fenerbahçe sun raba maki a wasan Istanbul Derby a wasan Victor Osimhen na farko bayan dawowar sa daga jinyan rauni.
Victor Osimhen ya shafe mintuna 90 a wasansa na farko bayan dawowar sa daga jinya, yayin da Galatasaray da Fenerbahçe suka buga kunnen doki a wasan Super Lig Istanbul Derby na farko a kakar wasa.

Dan wasan mai shekaru 26 ya dawo wasa a karon farko tun bayan raunin da ya samu a wasan da ya buga wa kasar sa Najeriya na neman shiga gasar cin kofin duniya.
Osimhen bai yi wasa kamar yadda ya saba ba amma ya buga mintuna casa’in na wasan da aka tashi kunnen doki.
Leroy Sane ya zura kwallo a ragar ƙungiyar Fenerbahce a gidan ta a minti 27, kusan rabin sa’a, kuma sun riƙe har zuwa ƙarshen wasan, kafin Jhon Duran ya farke kwallon a mintuna 90 a kayi 1-1.
Fenerbahçe ta yi ƙoƙarin samun nasara, amma Galatasaray ta riƙe, wanda hakan ya tabbatar da cewa ta ci gaba da kasancewa a saman teburin gasar, da maki ɗaya a kan abokan hamayyarta inda take da maki 33, Fenerbahce na matsayi na biyu da maki 32, bayan wasan mako na 14.


