Ranar Laraba ‘yan sandan kasar Finland suka kwace wani jirgin ruwa da ya taso daga Rasha, bisa zargin lalata wayoyin lantarki na tarho a karkashin ruwa, da suka taso daga Helsinki zuwa Estonia suka ratsa gulbin na Finland, gurin da a shekarun baya ya gamu da irin wannan barna.
Jirgin da aka kwace me suna Fitburg yana kan hanyar sa ne zuwa Isra’ila daga tashar ruwan Rasha ta St Petersburg, a lokacin da abin ya faru, a wata sanarwa da hukumar tsaron iyakar Finland ta yi wa manema labarai.
An shiga damuwa a Turai kan abin da jami’a suke gani karin barazanar daga Rasha tun lokacin da ta fara yaki da Ukrain, abin da ita Rashan ta karyata.


