Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta bayyana cewa ta kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a ayyukan masu garkuwa da mutane da kuma satar shanu a fadin jihar.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar dauke da sahannun Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Buhari Abdullah, an kama Abdullahi Ibrahim mai shekaru 40 a garin Tilde dake karamar hukumar Funakaye, a ranar 23 ga Nuwamba, 2025, bayan samun sahihan bayanai daga wani mai kishin kasa da suka zargeshi da boye masu laifi.
A yayin bincike, Abdullahi ya amsa laifin sa, inda ya bayyana cewa yana da hannu a satar shanu da kuma wasu hare haren masu garkuwa da mutane a fadin jihar Gombe.
Haka kuma ya fadi sunayen wasu abokan aikin sa da suka hada kai wajen gudanar da miyagun ayyukan a jihohin Gombe, Bauchi, Yobe da jihar Adamawa.
Rundunar ta ce a bisa wannan bayani ne jami’an ‘yan sanda da ke Operation Hattara tare da hadin gwiwar kungiyar masunta na jihar Gombe suka kai samame a wasu maboyar miyagun, inda aka yi musayar wuta da suka kai ga cafke karin mutum shida.
Wadanda aka kama sun hada da, Usman Mohammed, mai shekaru 30,Hussain Idris, mai shekaru 37, Adamu Tukur, mai shekaru 37 ,Yau Abdullahi, mai shekaru 25 da Ali Umar, mai shekaru 18 sai Hassan Usman, mai shekaru 40 da kuma Abdullahi Ibrahim, mai shekaru 40, daga Tilde,Karamar Hukumar Funakaye jihar Gombe
Sannan Rundunar ta tabbatar da ci gaba da gudanar da bincike tare da shirin gurfanar da su a gaban kotu.


