‘Yan bindiga sun hallaka Malaman makaranta a gundumar Filingue da ke yankin Tilabery iyakar Nijar da Mali.
Lamarin ya tada hankulan uwar kungiyar malaman makaranta wace ta yi kiran hukumomi su tsaurara matakai a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro donganin an ci gaba da karantarwa a makarantun boko.
Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da wadanan malamai da suka hada da darektan makarantar kauyen Sabon garin Takoussa Abdoulaye Askou da takwaransa na makarantar kauyen Maitalakia Nouhou Oumarou na kan hanyar zuwa taron kwamitin COGES da aka gudanar a Filingue lokacin da maharan suka afka masu kamar yadda kungiyar malaman kwantaragi ta SYNACEB ta bayyana a sanarwar nuna juyayi da ta fitar.
Wannan ba shi ne karon farko da ‘yan bindiga ke far wa malaman makaranta ba kokuma dakunan karantun da kansu a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro sabili kenan SYNACEB ke tunar da mahakunta a kan bukatar karfafa matakai domin dorewar sha’anin ilimi.
Kawo yanzu ba wata sanarwa daga bangaren gwamnati a kan wannan al’amari. Na tuntubi mai bai wa ministar ilimi shawara Issoufou Arzika ta waya to amma ya mayar da ni wajen jami’ar hulda da ‘yan jarida Hadiza Issa wace ba ta daga wayarta ba lokacin da na kira ta sannan ba ta amsa sakon text din da na tura ma ta har zuwa lokacin aika wannan rahoto.
Yankin Tilabery mai iyaka da Burkina Faso da Mali na daga cikin yankuna mafi fama da barazanar ‘yan bindiga lamarin da tun a wajejen 2017 ya haddasa rufe makarantu da dama koda ya ke a Watan satumban da ya gabata ministar ilimi Dr Elizabeth Cherif ta sanar cewa yawan irin wadanan makarantu ya ragu.
To amma ya mayar da ni wajen jami’ar hulda da ‘yan jarida Hadiza wace ba ta daga wayarta ba lokacin da na kirata sannan ba ta amsa sakon text din da na tura ma ta har zuwa lokacin aika wannan rahoto.


