Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana
Published: February 17, 2026 at 9:32 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ministan harkokin cikin gidan kasar Ghana ya bada labarin cewa ‘yan tawaye masu ikirarin Islama a Burkina Faso sun kashe ‘yan kasar Ghanan su bakwai masu cinikin tumatur, a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari kan wani gari da ake kira Titao dake arewacin Burkina Faso a ranar Asabar data gabata.

Mutanen da harin ya rutsa da su, suna cikin wata tawagar mutum 18 da suka shiga makwabciyar kasar daga arewa, domin su sari tumatur, lokacin da mayakan suka aukawa garin, suka rarrabe maza da mata, daga bisani suka bude musu wuta, kamar yadda ministan ya gayawa wata tashar gidan rediyon kasar.

Minista Mohammed Mubarak Muntaka yace “suka goce da harbe harbe, suka kashe kusan dukkan maza da suke wurin, suka kona gawarwakin su da babbar motar da suke ciki,” har ba’za iya shaida su ba.

Minista Muntaka yace maza uku da mace daya sun tsallake rijiya da baya tare da samun raunuka. Saura mata bakwai dake cikin ayarin sun tsere ba tare da sun jikkata ba.

Daga bisani ya dauki hukumomi a Burkina Faso sa’o’i masu yawa suka sake kwato iko kan garin, kamar yadda ministan ya fada, ya kara da cewa, jami’an na Burkina Fason, sunyi alkawarin bada kariyan soja ga sauran tawagar da wadanda suka jikkata zuwa ofishin jakadancin Ghana dake birnin Ouagadougou, babban birnin kasar ta Burkina Faso.

Afrika, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Dakarun Sojin Amurka Sunfara Sauka A Najeriya
Next Post: Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka

Karin Labarai Masu Alaka

Sabon Jagoran Addinin Iran Mojtaba Khameni Yaji Rauni Kuma Ya Nakasa Afrika
‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
Bincike Yanuna Kasashen Afirka Suna Cikin Mafiya Cin Bashi A Duniya Afrika
Hawan Sallah Daga Masarautar Misau Afrika
Sojin Israela Sunkai Hari Kan Falatsinawa Tsaro
Ana Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Djibouti Yau Juma’a Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jirgin Hakar Mai Daga Turkiyya Ya Isa Mugadishu
  • Farashin Mai Ya Doshi Dala 100 Kowacce Ganga
  • Shugaban Lebanon Ya Nemi Gudanar Da Shawarwari Kai Tsaye
  • Mataimakin Shugaban Amurka Ya Sauka A Islamabad Domin Tattaunawa
  • Iran Tace Dole A Tsagaita Wuta A Lebanon Kafun Fara Shawarwari

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shirin Dare 26.11.2025 Rediyo
  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda Afrika
  • Aminu Tambuwal Ya Fice Daga PDP Ya Koma ADC Afrika
  • Kasashen AES Sun Buɗe Gidan Talabijin Na Bai Daya Afrika
  • Bayan Shafe Shekaru Hudu A Mulki Sarkin Hausawan Ibadan Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • FIFA Ta Yi Wa Malaysia Kaca-kaca Wasanni
  • Shugaban Amurka Yace Zayyi Wahala A Cimma Yarjejeniya Tsakanin Isra’ila, Amurka Da Iran Amurka
  • Farashin Man Fetur Yakara Tashi Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.