Wani kwamiti na Majalisar Dinkin Duniya ya roki Britaniya da Mauritius da kada su rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da suka kulla game da makomar jerin tsibiran Chagos dake tekun Indiya, yana mai cewa yin hakan zai jaddada abinda aka jima ana yi ne na keta hakkin asalin mutanen wadannan tsibirai.
Wannan yarjejeniyar da aka kulla a watan Mayu, bayan da aka yi shekara da shekaru ana tattaunawa, zata mika iki da diyaucin wadannan tsibirai ga kasar Mauritius, amma zata kyale Britaniya ta ci gaba da iko da wani sansanin mayakan sama na hadin guiwa tsakaninta da Amurka, mai matukar muhimmanci, wanda suka gina a Diego Garcia, tsibiri mafi girma a jerin tsibiran na Chagos. Britaniya zata ci gaba da gudanar da sansanin karkashin wani tsari na haya na dogon lokaci.
A cikin shekarun 1960 da na 1970 an kwashe mutane dubu 2 karfi da yaji daga tsibiran, wasu da yawa suka koma Britaniya. Wasunsu sun nemi da su koma kasarsu ta asali.
Kwamitin Yaki da Wariyar Launin fata na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya gana a birnin Geneva, yace ya damu cewar wannan yarjejeniya ta fito a fili ta hana mutanen Chagos ikon komawa zuwa tsibirinsu na asali, Diego Garcia.


