Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Yau Shekaru 60 Da Kisan Gilla Ga Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato
Published: January 15, 2026 at 8:48 PM | By: Yusuf Aliyu Harande | Updated: January 15, 2026

Yau a ke cika shekaru 60 da yin kisan gilla ga Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto a juyin mulkin soja na farko a Najeriya.

Wasu hafsoshin soja daga akasari kabilar Igbo ne su ka aiwatar da juyin mulkin ranar 15 ga Janairu 1966.

Shi dai wannan juyin mulkin da ya haddasa zubar da jini ya yi sanadiyyar kisan gilla ga Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello, Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Balewa da Firimiyan kudu maso yamma Chief Ladoke Akintola a birnin Badun.

Juyin mulkin ya shafi manyan ‘yan siyasar Arewa da kuma Chief Akintola na Yarbawa amma bai taba kabilar Igbo ba.

Chukwuma Nzeogwu wanda hafsan soja ne da ya ci alfarmar Sardauna shi ya shiga gidan Firimiya ya yi ma sa kisan gilla shi da matarsa Hafsa da ta yi kokarin tare albarushi.

Nzeogwu ya nuna farin ciki da kisan da kuma mubaya’arsa ga Janar Johnson Aguiyi Ironsi wanda ya haye madafun iko a wannan yanayi na zubar da jini.

An tabbatar kalaman Sir Ahmadu Bello kan shirin ba wa al’ummar Arewa fifiko su amshi guraben ayyukan lardinsu da kaucewa babakeren Igbo ya zama daga dalilan kisan.

Dattijon NEPU da ta yi adawa da jam’iyyar NPC ta Sardauna Alhaji Hussaini Gariko ya ce adalcin Sardauna da amanarsa ababen koyi ne ga dukkan jagororin al’ummarmu.

Bayan kisan gilla Sardauna da Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Balewa, Janar Johnson Aguiyi Ironsi ya hau karaga amma kimanin wata 6 da kwana 15 a ka kifar de gwamnatinsa kuma har daga bisani ya kai ga yakin basasar Najeriya yayin da gwamnan Soja na jihar kudu maso gabar Odumegwu Ojukwu ya ayyana ballewa daga Najeriya.

Dakarun gwamnatin tarayya sun fafata tun daga 1967-1970 har su ka yi nasarar sake hade kasar.

Har yanzu Najeriya ba ta warware daga fitinar juyin mulkin 1966 ba.

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/01/AS-SARDAUNAS-ASSASSAINATION-CLOCKS-60-YEARS.mp3
Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Gabas Ta Tsakiya
Next Post: Tattalin Arzikin Najeriya Ya Farfardo Bisa Samun Wasu Sauye Sauye

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yansandan Uganda Sun Tsare ‘Yar Fafutukar Kare Hakkin Bil’adama Sarah Bireete Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Zamfara: Sai Mun Hada Kai Don Kawo Karshen Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ahmed Musa, Yayi Ritaya A ƙwallon ƙasa Da ƙasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Ribadu: Najeriya Ce Kasa Daya Tilo Da Ke Tabbatar Da Demokraɗiyya A Sahel Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Manchester United Ta Sallami Ruben Amorim Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Hukumar NDLEA Ta Kama Wata Mata Da cikin Bogi Na ƙwaya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar Zabe Ta Saukaka Gudanar Da Rijistar Katin Zabe A Najeriya Labarai
  • Dakarun Pakistan Da Afghanistan Sunyi Arrangama Labarai
  • Shugaban Rasha Yafara Ganawa Da Jakadun Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Ukraine Amurka
  • Kotu A Kasar Uganda Ta Bada Belin ‘Yar Gwagwarmaya Afrika
  • Kasar Congo Ta Dau Alwashin Bin Tsari Wajen Rarraba Ma’adanai Afrika
  • Bayan Shafe Shekaru Hudu A Mulki Sarkin Hausawan Ibadan Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Ukraine Tayi Watsi Da Shiga Kungiyar NATO Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.