Shugaba Zelensky na Ukraine ya bayyana bukatar ganawa da shugaba Trump, domin cimma matsaya dangane batutuwa masu sarkakiya da suka hada da iko kan wasu sassan kasar, a yunkurinda kasashen suke yi na kawo karshen yaki da kasar take yi da Rasha, sakamakon shawarwari da aka gudanar a baya bayan nan tsakanin jami’an Amurka dana Ukraine.
A cikin wata sanarwa da ofishin Mr. Zelensky ya baiwa manema labarai a a laraba, Mr. Zelensky yace tawagar jami’an kasarsa dana Amurka sun kusa kammala wani daftari dake kunshe da matakai daban daban har 20, a zaman shawarwari da suka yi a karshen makon jiya a birnin Miamai.
Shugaban Amurka Donald Trump ya juma yana fadin cewa yana son ganin an kawo karshen yaki mafi muni a Turai tun bayan yakin duniya na biyu, amma ya kasa samun hadin kai daga sassan dake gaba da juna a yakin na Rasha da Ukraine.


