Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamna Fubara: Rashin Kariya daga PDP Ne Ya Tilasta Ni Komawa APC
Published: December 10, 2025 at 4:54 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya ce barin jam’iyyar PDP da ya yi ya biyo bayan gazawar jam’iyyar wajen kare shi a rikicin siyasar jihar.

Fubara, wanda ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki a Fadar Gwamnati da ke Fatakwal, ya ce ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu ta tabbatar masa da cikakken goyon bayan da PDP ta kasa bashi.

Ya kuma tabbatar da komawarsa jam’iyyar APC tare da manyan magoya bayansa, yana mai cewa jam’iyyar ta ba shi kariya da goyon bayan da ake buƙata domin tsallake rikicin siyasar Rivers.

“Da ba don Shugaba Tinubu ya shiga tsakani ba, da babu Siminalayi Fubara a yau,” in ji shi, yana mai bayyana kudurinsu na mara wa Tinubu baya a tazarcen 2027.

  • Sauya sheƙar Fubara yana ƙara sauya yanayin siyasar Rivers, tare da yiwuwar yin tasiri a zabukan 2027 masu zuwa.
Siyasa

Post navigation

Previous Post: Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa
Next Post: Rikici Tsakanin NNPC Da Kungiyar Gwamnoni Akan Gibin Kudade

Karin Labarai Masu Alaka

Abba Kabir Yusuf Ya Koma Jam’iyar APC Siyasa
Iran Tace Jakadan Kasar Ta A Lebanon Zai Cigaba Da Zama A Beirut Afrika
Rikicin Siyasa A Jihar Rivers Sakamakon Ayyana Fubara A Matsayin Shugaban APC Siyasa
Ga Fili Ga Doki Dambarwar APC Da ADC Najeriya
PDP Ta Nemi Bincike Kan Rushewar Ginin Majalisar Dokokin Gombe, Tayi Zargi Game Da Sakaci Labarai
Gwamna Fubara Ya Koma Jam’iyar APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kuɗin 2026 Najeriya
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas Najeriya
  • Wata Biyu Najeriya Bata Bada Lasisin Shigo Da Mai Daga Ketare Ba Labarai
  • Mutum Mafi Tsufa A Saudiyya Ya Rasu Yana Da Shekaru 142 Labarai
  • Zamfara: Sai Mun Hada Kai Don Kawo Karshen Ta’addanci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NUJ: Akwai Bukatar Samar Da Inshorar Lafiya Ga ‘Yan Jarida A Najeriya Rediyo
  • Fiye Da Mutane 200 Sun Rasa Rayukansu A Wajen Hakar Ma’adanai Labarai
  • Masu Goyon Bayan Palasdinawa Sunyi Gangamin Zanga Zanga A Australia Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.