Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Soyinka Ya soki Yawan Jami’an Tsaron Da Ake Bai Wa Seyi Tinubu
Published: December 10, 2025 at 4:23 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Farfesa Wole Soyinka ya yi gargaɗi ga Shugaba Bola Tinubu kan yadda ake gudanar da tsaro da kuma amfani da jami’an gwamnati wajen kare wasu ‘yan tsiraru masu kusanci da fada.

Yayin bikin bayar da kyaututtuka na Wole Soyinka Centre for Investigative Journalism a Legas, a wani bidiyo da ya yadu, Soyinka ya ce ya yi mamakin ganin “babbar rundunar tsaro” da aka bai wa Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa, a Ikoyi.

Ya bayyana cewa yawan jami’an tsaron da ya gani “ya isa ya mamaye ƙaramar ƙasa,” lamarin da ya sa ya tuntubi mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, domin neman bayani.

Soyinka ya ce bai dace ‘ya’yan shugabanni su gaji karfin gwamnati ko su yi yawo da tsaro fiye da kima ba, yayin da ƙasar ke fama da hare-hare, garkuwa da mutane da rashin tsaro a sassa da dama.

Ya ƙara da cewa irin wadannan albarkatun tsaro ya fi dacewa a tura su wuraren da ake bukata, ba wajen kare masu gata ba.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: EFCC Ta Tsare Tsohon Minista Abubakar Malami
Next Post: Shugaba Tinubu Ya Umarci Janye ‘Yan Sanda Masu Gadin Ministoci

Karin Labarai Masu Alaka

NUJ Gombe Ta Ƙarfafa Bin Ɗa’a A Aikin Jarida, Ta Kaddamar Da Kwamitin Ladabtarwa Afrika
Hawan Sallah Daga Masarautar Misau Afrika
Atiku Ya Bukaci Hadin Kan ‘Yan Adawa Domin Kawo Sauyi A Najeriya Afrika
‘Yan Bindiga Sun Karya Alkawarin Dakatar Da Kai Hare Hare A Najeriya Labarai
Gombe Ta Yi Fice A Duniya: Maryam Dan’azumi Ta Lashe Gasar Alƙur’ani Na Ƙasa Da Ƙasa Afrika
Amurka Zata Bawa Sojojin Najeriya Horo Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • NFF Ta Nemi Afuwar Tinubu Da ’Yan Najeriya Kan Rashin Samun Tikitin Zuwa Gasar Kofin Duniya Ta Mata Wasanni
  • Shugaban Rasha Yafara Ganawa Da Jakadun Amurka Domin Kawo Karshen Yakin Ukraine Amurka
  • Shugaba Saied Yana Cigaba Da Samun Goyon Bayan Al’ummar Kasar Tunisiya Afrika
  • Nan Gaba Kadan Kwallon Badminton Zata Samu Karbuwa Kamar Kwallon Kafa A Duniya Labarai
  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini Afrika
  • Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba Afrika
  • Hawan Durba A Fadar Sarkin Zazzau Afrika
  • Real Madrid: Ta Kori Xabi Alonso Bayan Rashin Nasara A Wasan Kofin Sfaniya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.