Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Afrika
  • NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis Afrika
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika

Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa
Published: December 11, 2025 at 10:26 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kasar Iceland ta shiga cikin sahun kasashen Turai da zasu kaurace ma bikin gasar wakoki na Eurovision na shekara mai zuwa, bayan Kungiyar Masu Watsa Shirye ta Turai ta yarda zata kyale kasar Isra’ila ta shiga gasar.

Tun da fari shawarar kyale kasar Isra’ila ta shiga gasar Eurocision da za ayi cikin watan Mayu a Vienna ta kasar Austria, ta sa kasashen Spain, Netherlands, Ireland da kuma Slovenia sun janye daga shiga wannan gasa a saboda nuna rashin yarda da abubuwa da Isra’ila ta aikata a zirin Gaza.

Darakta janar na hukumar yada shirye-shirye ta kasar Iceland, Stefan Eiriksson, yace ganin irin muhawarar da al’ummar Iceland ke yi da kuma martaninsu ga shawarar kyale Isra’ila ta shiga cikin gasar, babu wani abin faranta rai ko kwanciyar hankali ga hukumar yada labarai ta kasar ta shiga cikin wannan gasa.

Iceland tana daga cikin kasashen da suka bukaci a jefa kuri’a tsakanin membobin kungiyar masu watsa shirye shirye ta Turai a kan batun shigar Isra’ila cikin gasar a makon jiya, amma sai kungiyar ta ki yarda da wannan, ta ce a maimakon haka ta fito da sabbin dokokin da zasu hana gwamnatoci yin katsalandan a gasar.

An fara gudanar da gasar Wakoki ta Eurovision tun a shekarar 1956, kuma a cewar kungiyar mutane miliyan 160 ke kallon gasar a akwatunan telebijin dinsu.

Labarai

Post navigation

Previous Post: An Kai Hari Da Jirgi Mara Matuki A Kusa Da Matatar Mai Din Kasar Sundan
Next Post: Gwamnatin Kano: Zamu Kara Daukar Malamai Domin Inganta Ilimi

Karin Labarai Masu Alaka

Isra’ila Zata Karbi Mutanenta A Yankin Gaza Labarai
Yohanna YD Buru: Makon Haɗin Kan Addinai Ya Ƙarfafa Ilimin Zaman Lafiya A Najeriya Labarai
EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran Afrika
APC: Tinubu Da Shettima Za Su Sake Neman Wa’adi Na Biyu A 2027 Afrika
Jam’iyyu Shida Sun Shiga Zaben Kananan Hukumomin Gombe – GOSIEC Afrika
Tarkacen Makamai Masu Linzami Sun Lalata Gidaje Da Wuraren Kasuwancin Palasdinawa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
  • NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Tinubu: Naji Dadin Sako Daliban Neja Da Aka Sace Labarai
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya Rusa Majalisar Zantaswa ta Jihar Gombe Labarai
  • Addini Ko Kabilanci Basu Da Gurbi Cikin Ta’addanci Labarai
  • Mutane 13 Sun Mutu Inda Wasu 57 Suka Jikkata A Barundi Afrika
  • Najib Razak Zai Kara Shekaru 15 A Gidan Yari Saboda Cin Zarafin Kujerar Mulki Labarai
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Rasha: Zamu Ba Gwamnatin Venezuel Gudunmawa Sauran Duniya
  • Jama’ar Kasar Iran Sun Bayyana Goyon Baya Ga Ayatollah Mojtaba Khameni Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.