Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Majalisar Wakilai Ta Rikon Kwaryar Nijar Ta Gudanar Da Zama Karo Na Biyu
Published: December 17, 2025 at 3:05 AM | By: Yusuf Aliyu Harande

Majalissar wakilai ta rikon kwaryar jamhuriyar Nijar ta fara zamanta na biyu na karshe a shekarar nan ta 2025.
A tsawon kwanaki biyu na wannan zama wakilan zasu tattauna batutuwa da dama da suka shafi tafiyar kasar kamar yadda  gwamnatin mulkin sojan kasar ta shigar da bukata. Sai dai wasu ‘yan kasar sun shawarci majalissar a kan wasu karin batutuwan da ke bukatar matakan gaggawa.
 Taron Wanda ke matsayin na rufe shekarar nan ta 2025 lokaci ne da wakilai 194 na majalissar ta conseil consultatif de la refondation zasu nazarci kudirorin da gwamnatin ta Nijar ta zo da su da suka shafi fannoni da dama.
Farfesa Dicko Abdourahamane na daga cikin mahalarta taron.
Kundin tsarin mulkin gwamnatin ta rikon kwarya da ya samo asali daga babban taron rukunonin al’ummar kasar ya bai wa majalissar hurumin sauraren mimbobin gwamnati idan bukatar hakan ta taso saboda haka a wannan karon za su mori wannan dama kamar yadda shugaban kwamitin kula da siyasar duniya a majalissar CCR Bana Ibrahim ya bayyana.
Duk da cewa zaman na da mahimmanci a wajensu wasu ‘yan Nijar kamar su Salissou Ibrahim na FRSA na jan hankula a kula da wasu abubuwan da a cewarsa suna kan gaba a jerin manufofin shugaban kasa.
Shi kuma shugaban kungiyar yaki da cin hanci ta RENAC kwararre kan sha”anin shugabanci Adamou Oumarou na kokarin ankarar da zaman na wannan karon kan matakan taka birki daga yunkurin ciyo bashi daga waje.
A karshen taron na kwanaki 15 majalissar ta CCR za ta gabatar da takardun shawarwari wa bangaren zartarwa inda Janar Abdourahamane Tiani da ke da maganar karshe zai yi na’am kokuma ya bukaci majalissar ta yi Zaman gaggawa don kwaskware abinda ke bukatar gyara.
TARON MAJALISSAR WAKILAI
Afrika

Post navigation

Previous Post: Cutar Zazzabin Lassa Tayi Ajalin Mutum 1 Yayinda Mutane 11 Suka Kamu A Jihar Gombe
Next Post: Wani Jirgi Yayi Saukar Angulu Ba Shiri

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa Afrika
Gwamnatin Jihar Filato Ta Sauke Hakimin Mushere Afrika
Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Kashe Mutane Biyar A Tanzaniya Afrika
Meyasa Israela Take Hana Kaiwa Gaza Kayan Tallafi Afrika
Kotu A Najeriya Ta Kame Mutane Bisa Zargin Ta’addaci Afrika
Kotu Tayi Watsi Da Tarukan ADC Bangaren David Mark Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Anfara Gangamin Kafa Dokoki Masu Tsanani Ga ‘Yan Luwadi A Senegal Afrika
  • ‘Yan Tawayen M23 Masu Samun Goyon Bayan Rwanda Basu Jamye A Ulvira Ba Labarai
  • Iran Tabada Tabbacin Cigaba Da Rufe Mashigar Hormuz Afrika
  • Trump Yace Amurka Ta Kai Hare-Hare Masu Yawa Akan ‘Yan Ta’adda A Najeriya Amurka
  • Kasashen Duniya Sunyi Tir Da Hambarar Da Gwamnatin Venezuela Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya Ta Kai Wasan Kusa Da Na Karshe A Wasan Dambe Na Matasan Afirka Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.