Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Jihar Yobe: Ana Cin Zarafin Fursunoni A Gidan Gyaran Halin Potiskum
Published: December 17, 2025 at 11:29 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar da samuwar wata ƙungiyar dake lalata tare da cin zarafin fursunoni a Gidan Gyaran Hali na Potiskum.

Mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Abdulsalam Abubakar mai ritaya, ne ya bayyana hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron Majalisar Tsaron Jihar da aka gudanar a ranar Talata a Damaturu.

Abdulsalam ya bayyana lamarin a matsayin babbar cin amana, inda ya ce ana zargin wasu jami’an gidan yari da yi wa wata fursuniya ciki a cikin gidan gyaran halin.

Ya ce hakan na nuna sakaci wajen aiki da kuma rashin kulawa yadda ya kamata, yana mai cewa a ka’ida babu yadda za a yi jami’in tsaro namiji ya shiga sashen mata idan ana sa ido yadda ya dace.

Mai ba da shawarar kan tsaro ya ce, bincike na ci gaba da gudana, inda ya kara da cewa har yanzu ba a tantance adadin jami’an da ke da hannu a lamarin ba, domin ana ci gaba da kama wasu da ake zargi inda ya kara da cewa, al’amarin wata ƙungiya ce mai faɗi, bawai mutum ɗaya ba, kuma akwai masu taimaka musu ciki har da wasu jami’an mata.

Sai dai Abdulsalam ya nuna fatan cewa duk wanda aka samu da laifi a binciken da Hedikwatar Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa ke gudanarwa, za a miƙa shi ga ‘yan sanda domin gurfanar da shi a gaban kotu.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta riga ta kai ƙorafi ga shugabancin Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa da Ma’aikatar Harkokin Cikin gida yana mai jaddada cewa gwamnati na da alhakin kare rayuka, dukiya da mutuncin al’umma.

A game da samar da tsaro lokacin bukukuwan Kirsimeti, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Emmanuel Ado, ya ce an shirya tsaro sosai, inda aka tura jami’ai da dama zuwa wuraren ibada da wuraren shakatawa.

Ya tabbatar wa mazauna jihar, musamman mabiya addinin Kirista, cewa za su gudanar da bukukuwansu cikin kwanciyar hankali ba tare da fargaba ba.

Tsaro

Post navigation

Previous Post: Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi
Next Post: Gwamnatin Gombe Zata Inganta Samar Da Wuta Wajen Amfani Da Hasken Rana

Karin Labarai Masu Alaka

An Saka Dokar Hana Fita A Jos Ta Arewa Afrika
An Karrama Darakta Janar Na DSS Bisa Ƙoƙarinsa Na Inganta Alaƙar Hukumomin Tsaro Da Kafafen Yaɗa Labarai Afrika
‘Yan Kasashen Afirka Da Dama Suna Fafatawa Da Rasha A Yaki Da Ukraine Afrika
Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai Amurka
Hukumar Ƴan Sanda Ta Musanta Zargin Kashe Ɗan Achaba a Gombe Tsaro
Majalisar Dinkin Duniya Ta Amince Da Kudurin Kasar Ghana Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ronaldo Da Messi Ka Iya Hadu A Gasar Cin Kofin Duniya: Ta Ya Ya ? Wasanni
  • Kungiyar ‘Yan Ta’adda Masu Alaka Da ISIS Sun Kashe Mutane A Congo Tsaro
  • Najeriya Da Kasar Saudiya Sun Kulla Yarjejeniyar Tsaro Labarai
  • Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
  • Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Wutan Lantarki A Jami’ar Bayero Afrika
  • Malami: “Da Gwamnatin Tarayya Na Daukar Shawara Da Ba’a Kai Inda Ake Ba” Najeriya
  • Rasha Ta Nuna Kudurin Cimma Zaman Lafiya Da Ukraine Amurka
  • ‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.