Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila
Published: December 23, 2025 at 9:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da korar Adamu Abdullahi Danko da wasu mataimaka uku nan take bayan binciken cin zarafin da aka yiwa, Abdulrahman Abubakar Sheriff, Kansila mai wakiltar gundumar Shamaki a karamar hukumar Gombe.

Matakin wadda Sakataren Gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya sanar, ya biyo bayan kafa kwamitin bincike na musamman ne kan lamarin.

Sakamakon binciken kwamitin wanda rahotannin hukumomin tsaro suka tabbatar ne ya kai ga matakin da Gwamnan ya ɗauka.

A cewar Sakataren Gwamnatin Jihar, masu taimakawa gwamnan da abin ya shafa sune, Adamu Abdullahi Danko – Babban Mataimaki na Musamman na 2 kan Harkokin Cikin Gida, da Garba Mohammed Mai Rago – Babban Mataimaki na Musamman na 2 kan harkokin Siyasa, da Rabiu Sulaiman Abubakar – Babban Mataimaki na Musamman na 2 kan Kafafen Sada Zumunta na Zamani da kuma Ali Ibrahim Baban Kaya – Babban Mataimaki na Musamman na 2 kan Hulɗa da al’umma.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bada umarnin cewa korar ta fara aiki ne nan take.

An kuma umurci duk jami’an da abin ya shafa su miƙa duk kadarorin gwamnati dake hannunsu ga hukumomin da suka dace ba tare da wani ɓata lokaci ba.

Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci tashin hankali, rashin ɗa’a da cin zarafi ba, yana mai cewa ba zai lamunci duk abinda zai iya yin barazana ga zaman lafiyar jama’a ko lalata amincin da gwamnatinsa ke da shi a idon al’ummar jihar ba.

Ya tabbatarwa al’ummar jihar Gombe jajircewar gwamnatinsa wajen tabbatar da bin doka da oda, riƙon amana da kuma zaman lafiya sannan ya ƙara da cewa za a ɗauki matakai masu tsauri don kare zaman lafiya da ɗorewar kwanciyar hankalin da jihar take ta fafutukar ɗabbaƙawa.

Najeriya

Post navigation

Previous Post: Sojin Ukraine Sun Janye Daga Gabashin Kasar
Next Post: Babban Hafsan Sojan Libya Ya Mutu A Wani Hatsarin Jirgin Saman Turkiyya

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Sanatan Nasarawa Ta Arewa Ya Rasu A Kasar India Najeriya
NAHCON Tafara Shirye-Shiryen Aikin Hajjin 2026 Najeriya
NNPC Da Wasu Kamfanoni Sunyi Yarjejeniyar Iskar Gas Najeriya
Jihar Borno Ce Tayi Nasara A Gasan Karatun Al Qur’ani Na Kasa Najeriya
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Hadakar Ta Da Amurka Wajen Yakar ‘Yan Ta’adda Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Kyautata Dangantaka Tsakanin Jami’an Tsaro Da Al’umma Ce Mafita Najeriya
  • Shugaban Najeriya Bola Tinubu Zai Ziyarci Jihohin Borno,Bauchi Da Legas Labarai
  • Jirgin Sama Ya Fadi A Kano Labarai
  • Rasha Da Ukraine Sun Cigaba Da Yakar Juna Afrika
  • Ansamu Girgizar Kasa A Kasar Taiwan Labarai
  • Akwai Yiwuwar Shugaban Ƙasar Afirka Ta Tsakiya Touadera Yasamu Nasara A Karo Na Uku Afrika
  • Fadar Shugaban Ƙasan Najeriya Ta Musanta Wani Labarin ƙarya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kanal Sani: Idan ‘Yan-Ta’adda Zasu Mutunta Sulhu To Gwamnati Ta Duba Hakan Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.