Kotun FCT Abuja ta bayar da belin wucin gadi ga Abubakar Malami, ta dage sauraron shari’a zuwa 5 ga Janairu
Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja Najeriya ta bayar da belin wucin gadi ga tsohon Babban Lauyan kasar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a shari’ar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ke gabatarwa a kansa.
Mai shari’a Bello Kawu ne ya yanke wannan hukunci a ranar Talata, 23 ga Disamba, 2025, yayin sauraron ƙarar mai lamba M/17220/2025.
Kotun ta ce an bayar da belin ne bisa sharuddan da EFCC ta riga ta gindaya tun farko, waɗannan sun haɗa da mika fasfo ɗin tafiyar ƙasashen waje na Malami, tare da cike takardun beli daga mutane biyu masu tsaya masa.
Mutanen da za su tsaya masa su ne Daraktan Janar na Hukumar Tallafin Shari’a ta Ƙasa (Legal Aid Council) da kuma ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Augie/Argungu.
Mai shari’a Kawu ya kuma sake dubawa tare da farfaɗo da sharuɗɗan belin da aka riga aka cika tun 28 ga Nuwamba, 2025, ciki har da mika fasfo da kuma gabatar da mutanen da za su tsaya masa.
Kotun ta bayyana cewa an bayar da belin wucin gadin ne bisa dalilin tsananin wahala ta musamman, har zuwa lokacin da za a saurara kuma a yanke hukunci kan babbar ƙarar da ke gaban kotu.
An dage sauraron shari’ar zuwa 5 ga Wata Janairu, 2026, domin jin ƙarar a hukumance.


