Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry
Published: December 31, 2025 at 5:29 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Sakamakon wacin gadi da aka bayar na zaben shugaban kasa a Guinea-Conakry ya nuna cewa madugun juyin mulki Mamady Doumbouya, shine ya lashe zaben da gagarumin rinjaye

Sakamakon na wucin gadi da aka sanar ranar talata ya nuna cewa Doumbouya ya samu kusan kashi 87 daga cikin 100 na kuri’un da aka jefa ran 28 ga watan nan na Disamba, rinjayen da ya sa ba ma sai an sake zaben fitar da gwani ba.

Kotun kolin kasar tana da kwanaki 8 domin tabbatarwa ko kin tabbatar da wannan sakamako idan an samu wanda zai kalubalance shi.

Da ma dai ana sa ran Doumbouya zai lashe wannan zabe da zai ba shi wa’adin shekaru 7 a kan kujerar shugabancin kasar.

Tsarin mulki na farko da aka bayar a kasar Guinea Conakry a bayan juyin mulkin Doumbouya na 2021, ya haramtawa shugabannin sojoji tsayawa takara a zaben, amma a watan Satumba an gudanar da kuri’ar raba gardama a kan wani tsarin mulkin wanda yayi watsi da wannan tanadi.

Kasar Guinea-Conakry ta fi kowace kasa a duniya arzikin karfen goran ruwa da kuma bakin karfe.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Wasu Muhimman Abubuwa Da Najeriya Ba Zata Manta Da Su Ba A 2025
Next Post: Kasashen Mali Da Burkina Faso Sun Haramtawa Amurkawa Shiga Kasashen

Karin Labarai Masu Alaka

Sojin Saman Najeriya Sun Lalata Sansanonin ‘Yan Ta’adda Afrika
Kasar Ghana Ta Bayyana Fataucin Bayi A Matsayin Babban Laifi Afrika
Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan Labarai
Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika
China Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Kulla Yarjejeniya Afrika
Kotu A Kasar Tunisiya Ta Daure Wani Babban Dan Kasuwa Da Wasu ‘Yan Majalisa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rundunar Sojin Najeriya Ta Kubutar Da Wasu Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Dasu Afrika
  • Yakin Rasha Da Ukrain Babban Kalubale Ne Ga Kasashen Turai Labarai
  • Jirgi Marar Matuki Yayi Ajalin A Kallah Mambobin M23 9 Tare Da Kashe Kakakin Rundunar Afrika
  • NFF, Ta Umarci Tawagar Masu Horas Da Super Falcons Su Sauka Daga Bakin Aiki Nan Take Wasanni
  • Ministocin Kasar Asia Zasu Gudanar Da Taro A Kasar Malaysia Tsaro
  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Jam’iyyu Shida Sun Shiga Zaben Kananan Hukumomin Gombe – GOSIEC Afrika
  • Mabiya Addinin Kirista Da ‘Yan Bindiga Suka Sace Sun Kubuta Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.