Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Kasashen Mali Da Burkina Faso Sun Haramtawa Amurkawa Shiga Kasashen
Published: December 31, 2025 at 5:36 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kasashen Mali da Burkina Faso sun ba da sanarwa da maraicen talatar nan cewa zasu haramtawa Amurkawa shiga cikin kasashensu, domin maida martani ga matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na haramtawa ‘yan kasashen biyu shiga kasar Amurka.

Wannan matakin da ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka bayar da sanarwarsa a lokuta daban daban, ya nuna irin yadda dangantaka ta yi tsami a tsakanin gwamnatocin mulkin soja na kasashen Afirka ta Yamma da kuma Amurka.

A ranar 16 ga watan Disamba ne shugaba Trump ya fadada takunkumin hana wasu ‘yan kasashen waje izinin shiga Amurka inda ya hada da kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar, wadanda gwamnatocin su suka balle daga Kungiyar ECOWAS ko CDEAO suka kafa ta su ta Kungiyar Kasashen Yankin Sahel.

Tun da fari, gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar daukar irin wannan matakin ramawa kura aniyarta, ta ce ta haramtawa dukkan Amurkawa shiga cikin kasarta.

Afrika

Post navigation

Previous Post: Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry
Next Post: An Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Somaliya

Karin Labarai Masu Alaka

Kimanin Mutane 200 Ne Suka A Mutu A Wani Harin Jirgin Yakin Sojin Najeriya Afrika
Amurka Da Iran Sun Tattauna A Kasar Pakistan Afrika
Gwamna Abba Kabir Ya Zabi Garo A Matsayin Mataimaki Afrika
Papa Roma Leo Yace Zai Cigaba Da Sukan Yake Yake Afrika
Isra’ila Tace Bazata Sake Kai Hari Kan Cibiyar Gas Ta Iran Ba Afrika
Dillalan Mai Suna Fuskantar Karancin Mai Sakamakon Yakin Amurka Da Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 33 Bisa Zargin Kai Hari A Jihar Kwara Afrika
  • Kasar Tanzaniya Zata Gina Babban Tashar Iskar Gas Labarai
  • Jami’ai A Afirka Sunce Tashin Farashin Mai Kalubale Ne Ga Tattalin Arziki Afrika
  • Afirka Ta Kudu Ta Samu Rigakafin Cutar Boro Afrika
  • Barcelona Ta Lashe Kofin Spanish Super Cup  Wasanni
  • Nigeria Zata Bude Asusun Dala Bilyan Biyu Don Habaka Sashin Makamashi Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Tana Saka Ido Akan Matsalolin Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • RUWASSA Ta Hada Masu Ruwa Da Tsaki Domin Inganta Aiwatar Da Shirin NG-SURWASH Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.