A Afirka ta kudu darajar kudin kasar da ake kira Rand ya tashi da kamar kashi 13 ckin dari a bara idan aka kwatanta da dalar Amurka, wanda ya nuna karin da darajar kudin kasar ya samu cikin shekaru 16 kan dalar Amurka, a dai dai lokacin da darajar kudin Amurka yake faduwa.
Ana alakanta wannan nasarar ce kan ci gaba da Afirka ta kudu ta samu wajen shawo kan hauhawar farashi da kuma karin kudaden shiga da kasar ta samu daga albarkatun kasa kamar Zinari da ma’adinai da ake kira Platinum farashin su ya tashi sosai a bara.
Sabanin haka, darajar dalar Amurka ta fadi da kamar kashi 9 cikin dari a shekarar da ta kare ranar laraba, wanda shine koma baya mafi tsanani da dala ta fuskanta cikin shekaru takwas da suka wuce.
Wadda haka ya jibanci kiran babban bankin Amurka ya rage kudin ruwa, da damuwa da ake nunawa kan tulin bashi da yake kan Amurkan, da kuma rashin tabbas kan makomar harkokin siyasar kasar.
Wadannan dalilai ne suka sa farashin zinari da wasu albarkatun kasa suka tashi wadanda ake amfani da su a zaman wurin adana dukiya, yasa farashin zinari ya haura dala dubu hudu kan ko wani ma auni a watan oktoba, sama da shekaru 40 rabon da aga farashin zinari ya kai haka.
A bara ne ya cika shekara daya da gwamnatin hadin guiwa a Afirka ta kudu, wadda takaddama kan kasafin kudi, da kuma damuwa kan haraji mai yawa da shugaban Amurka Donald Trump ya azawa kasar suka dauke hankali ta fuskar tattalin arziki.


