Akalla mutane 25 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 13 suka jikkata sakamakon hatsarin jirgin ruwa da ya faru a yankin Nguru, jihar Yobe a Najeriya.
Wasu mazauna yankin sun bayyana yadda jirgin ya nutse a tsakiyar ruwa, lamarin da ya sa fasinjoji da dama suka shiga cikin haɗari kafin a samu agaji.

Waɗanda suka tsira daga hatsarin sun shaida cewa, cikin tsoro da tashin hankali, mutane da yawa sun yi ta neman yadda za su ceci kansu, yayin da wasu ke faman taimakawa waɗanda suka fada cikin ruwa.
An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Babban Asibitin Nguru domin samun kulawa, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike don gano ainihin musabbabin hatsarin.



