Gidan telebijin na Masar yace kasar ta rattaba hannu a kan yarjejeniyoyi na kudi dala miliyan dubu daya da dari takwas na samar da makamashi ta hanyoyin da ake iya sabuntawa.
Daga cikinsu har da wasu takardun kwantaraki da wani kamfanin kasar Norway mai suna SCATEC da kuma kamfanin Sungrow na kasar China.
Masar tana fatan samar da kashi 42 cikin 100 na wutar lantarkinta ta makamashin da ake iya sabuntawa nan da shekarar 2030.
Kamfanin SCATEC zai gudanar da aikin farko na kafa tashar samar da wutar lantarki daga hasken rana tare da tashoshin adana wutar lantarkin a Minya dake arewacin Masar kuma wannan tasha zata iya samar da Gigawatt 1.7 na wutar lantarki, inda za a yi amfani da baturan tara wuta da zasu iya tara gigawatt 4.
Aiki na biyu shine wanda kamfanin Sungrow na China zai yi na gina masana’antar kera baturan adana wutar lantarki a yankin Suez.


