Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula
Published: January 15, 2026 at 3:56 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 15, 2026

Rundunar sojojin kasar Sham ta ce yau alhamis zata bude hanya domin fararen hula su fice daga wani yanki na lardin Aleppo da ake kara jibga sojoji cikinsa, a bayan kazamin fada da aka gwabza tsakanin dakarun na gwamnati da na Kurdawan cikin birnin Aleppo.

Wannan sanarwa da rundunar sojojin ta fitar cikin daren laraba, wadda ta ce fararen hula na iya ficewa ta hanyar da za a bude daga karfe 9 na safiya zuwa 5 na yamma agogon kasar, tana nuna alamun cewa ana shirin kai farmaki a garuruwan Dar Hafer da Maskana da yankunan dake kewaye da nan, masu tazarar kilomita 60 a gabas da birnin Aleppo.

Rundunar sojojin ta yi kira ga dakarun kungiyar SDF dake karkashin jagorancin Kurdawa da ta janye mayakanta zuwa tsallaken kogin al-Furat, wato zuwa gabas da inda ake takaddama a kai.

Tuni dai rundunar sojojin Sham ta tura karin dakaru zuwa yankin, a bayan da ta ce kungiyar SDF ma tana ta kara jibge sojojinta a wurin.

Gwamnati ta zargi kungiyar SDF da laifin kai hare-hare da jiragen drone na birnin Aleppo, ciki har da wani hari kan ginin gwamnatin lardin Aleppo jim kadan a bayan da wasu ministoci biyu suka yi hira da ‘yan jarida.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan
Next Post: Kasar Amurka Da Denmark Suna Rikici Akan Iyakar Greenland

Karin Labarai Masu Alaka

Ghana Ta Haramta Hakar Ma’adinai A Gandunan Dajin Data Kebe, Labarai
Kama Muhyi Magaji Siyasa ce Kawai Inji Gwamnatin Kano Labarai
Iran Ta Kama Wani Jirgin Ruwa Shake Da Mai Labarai
Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Aika Sammaci Dr. Yusuf Baba-Ahmed Labarai
An Yanke Hukuncin Kisa Ga Hasina Tsohuwar Firaiy-Ministan Bangladash Labarai
Baba Buhari Yayi Zargin Ansaka Masa Na’urar Tsaro Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Gabas Ta Tsakiya
  • Kasar Amurka Da Denmark Suna Rikici Akan Iyakar Greenland
  • Kasar Sham Ta Sallami Wasu Fararen Hula
  • Zaman Lafiya Yafara Dawowa A Sudan
  • Shugaban Kasar Uganda Yana Kokarin Mayar Da Mulkin Kasar Na Gado

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Kotun Tarayya Ta Yankewa Nnamdi Kanu Daurin Rai-da-Rai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Gudanar Da Taron Matasan Kasashe 6, Don Kawo Karshen Ta’addanci Wasanni
  • An Sako Ɗaliban Makaranta 130 Da Aka Sace A Jihar Neja  Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Fubara Yana Yiwa Dimokraɗiyya Zagon Kasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Kimanin Ganga Miliyan 40 Na Danyen Albarkatun Mai Yayi Kwantai A Kasashen Afirka Ta Yamma Afrika
  • Kasar Belarus Zata Taffawa Jamhuriyar Nijar Afrika
  • Shugabar Hamayya A Venezuela Ta Gana Da Paparoma Leo Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.