Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi Afrika
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe Afrika

Limamin Da Ya Ceci Kiristoci Lokacin Rikicin Addini A Jihar Filato Ya Rasu
Published: January 16, 2026 at 12:16 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 16, 2026

Limamin addinin Islama daya ya sami shahara har ya sami lambobin yabo kan zaman lafiya a jahar Filato, Imam Abdullahi Abubakar ya rasu a Jos.

Marigayi Imam Abdullahi Abubakar ya shahara a duniya ne biyo bayan sadaukar da kai da yayi na bada kariya ga mabiya addinin Kirista fiye da dari uku, bayan ‘yan bindiga sun kai musu hari a kauyen Yalwan Gindin Akwati dake karamar hukumar Barkin Ladi a shekarun baya.

A ranar Alhamis goma sha biyar ga watan Janairun dubu biyu da ishirin ta shida, da misalin karfe tara na dare ne, Allah ya karbi ran Imam Abdullahi Abubakar bayan fama da rashin lafiya.

Malamin, wanda yayi limanci a karkara, musamman a yankin da a baya ake samun yawan tashin hankali, ya taimaka kwarai wajen wanzadda zaman lafiya da hadin kai tsakanin mabiya addinai da kabilu daban-daban, wanda ya kai ga har kasashen duniya irin su Amurka da Saudi Arebiya da kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatocin tarayya da na jahar Filato suka bashi lambobin yabo da adadinsu ya kai goma sha hudu.

A zantawarsa da wakiliyar GTA Hausa a Jos, Zainab Babaji, kafin rasuwarsa, Imam Abdullahi Abubakar ya bayyana cewa yana sauke hakkinsa na zama da kowa lafiya ne, kamar yadda Allah ya hori al’umma suyi, don haka ya sadaukar da ransa wajen ceton Kirista fiye da dari uku, a lokacin da ‘yan bindiga suka mamayesu.

Imam yace a dalilin ayyukan zaman lafiya da yayi, ya sami lambobin yabo, ya kuma je aikin Hajji banda ganawa da yayi da manyan shugabannin duniya ciki har da marigayi, shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da wassu gwamnoni.

Malam Abdullahi Umar Hassan, na’ibin limamin masallacin da Imam Abdullahi Abubakar ya jagoranta, ya bayyana mamacin a matsayin mai son hada kan jama’a ba tare da nuna bambanci ba.

Malam Hassan yayi fatar Allah ya zabo wanda zai cike gurbin da Imam ya bari na wanzadda zaman lafiya.

Haka ma kafafen sada zumunta a yau Jumma’a sun cika da hotunan Imam Abdullahi Abubakar, musammman daga wadanda suka yi hulda dashi a lokacin da yake raye, suna bayyana alhininsu kan rashin dattijon, da zayyana irin ayyukan alkhairi da yayi na samadda zaman lafiya.

Ga Rahoton Zainab Babaji Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/01/AUD-20260116-WA0025.mp3
Labarai

Post navigation

Previous Post: Dan Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya Atiku Abubakar Ya Shiga Jam’iyyar APC
Next Post: Ana Zargin Wani Dan Kasar Libya Da Fataucin Mutane

Karin Labarai Masu Alaka

Hukumar Tsaron Civil Defence A Gombe Ta Samar Da Jami’ai Don Tabbatar Da Tsaro A Bukukuwan Karshen Shekara Labarai
Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
Gwamnatin Najeriya Ta Horar Da Matasa Sama 7,000 A Matsayin Masu Tsaron Daji Labarai
Isra’ila Ta Dau Alwashin Kawo Karshen Falasdi Labarai
Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari Afrika
Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani
  • Jami’an ‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayi
  • Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai
  • Najeriya Da Jamus Sun Kulla Yarjejeniyar Zuba Jari
  • Zaben Fidda Gwani Ya Gudana Lafiya A Jihar Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Tinubu Ya Yi Allah Wadai Da Kashe-kashen Jos Da Kaduna Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Taya Super Eagles Murnar Lashe Tagulla A Gasar AFCON Wasanni
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana Afrika
  • Shugaba Trump Ya Bukaci Kasar Iran Ta Mika Wuya Amurka
  • Wani Dan Bindiga Ya Harbi Dakarun Tsaron Cikin Gida Su Biyu A Washington DC Labarai
  • Farashin Kasuwar Yawon Bude Ido A Kasuwar Hannayen Jari Ya Fadi Afrika
  • Kasar Ghana Ta Bayyana Fataucin Bayi A Matsayin Babban Laifi Afrika
  • Tsohon Lauyan Amurka Jack Smith Ya Fadi Maganganu Game Da Donald Trump Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.