Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

‘Yan Kasar Cuba Sunyi Zanga Zanga A Ofishin Jakadancin Amurka
Published: January 16, 2026 at 10:11 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Dubbannan ‘yan kasar Cuba sun yi zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Amurka da ke Havana don nuna kin amincewa da mulkin kama karya da Amurka ke yi a yankunan su, biyo bayan kame shugaban Venezuela Niclas maduro.

Zaman doya da manjan da aka dade ana yi tsakanin Amurka da Cuba ya kara ta’azzara ne tun bayan da Amurkan ta kai farmaki Kasar Venezuela da yayi sanadiyar sojoji da jami’an leken asiri na Cuba 32, da ke bawa Maduro kariya, wannan ita ce karawa ta farko tsakanin sojin Amurka da na cuba cikin shekaru da dama.

Da yake jawabi ga masu zanga-zangar, yana me juya bayan sa ga ofishin jakadancin Amurka, shugaban kasar Cuba Miguel Diaz, sanye da Kayan soja, ya yi kira ga ‘yan kasar su ci gaba da hadin kai a yayin da ake fuskantar matsi daga Amurka.

Ya ce, masu mulkin mallaka, bama tsoron ku, kuma bama so ayi mana barazana, a yayin da ya juya yake nuna ofishin jakadancin da yatsa, ya kara da cewa ba zaku razana mu ba.

Ranar Lahadin da ta gabata ne, shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba wani man fetur ko kudi na Venezuela da zai kara shiga hannun Cuba, inda ya gargadi fadar gwamnatin Havana ta yi yarjejeniya kafin lokaci ya kure mata.

Amurka

Post navigation

Previous Post: Ana Zargin Wani Dan Kasar Libya Da Fataucin Mutane
Next Post: Kasar Canada Ta Amince A Shigar Da Motoci Kirar Kasar China Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Farashin Mai Ya Ragu A Kasuwar Duniya Amurka
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ta Saka Takunkumi Visa Ga Wasu ‘Yan Rwanda Afrika
Shugaba Donald Trump Yabada Umarnin Hana Jiragen Dakon Mai Shiga Venezuela Amurka
Farashin Dalar Amurka Ya Tashi Ranan Juma’a Amurka
Kasar Canada Ta Amince A Shigar Da Motoci Kirar Kasar China Kasar Amurka
Farashin Zinari Yayi Tashin Gwauron Zabi Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shirin Ga Fili GA Doki Shirye-Shirye
  • Lakurawa Sun Kashe A Ƙalla A Mutane 34 A Jihar Kebbi Labarai
  • Dalibai Sun Koma Makarantu A Wasu Jihohin Najeriya Najeriya
  • ‘Yan Sanda A Finland Sun Kwace Jirgin Ruwan Kasar Rasha Afrika
  • Jihar Borno Ce Tayi Nasara A Gasan Karatun Al Qur’ani Na Kasa Najeriya
  • Mutane Kusan 30 Ne Suka Mutu a Nguru Dake Jihar Yobe Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Matsalolin Masarautun Kano Sun Kawo Karshe Najeriya
  • Ukraine Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Tsarin Cimma Yarjejeniya Sauran Duniya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.